PDP ta yi martani kan durkusawa da El-Rufai ya yi yana rokon al'umma su yi wa Yahaya Bello afuwa

PDP ta yi martani kan durkusawa da El-Rufai ya yi yana rokon al'umma su yi wa Yahaya Bello afuwa

Jam'iyyar PDP ta ce durkusawa don nema wa Gwamna Yahaya Bello da shugaban kamfe din jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Kogi, Nasir El-Rufai ya yi alama ce dake nuna ya amince da cewa Yahaya Bello bai cancanta ya zarce ba.

Gwamna El-Rufai ya durkusa gaban al'ummar Kogi yana rokon su yafe wa Gwamna Yahaya Bello kurakuren da ya yi. Ya yi hakan ne yayin yakin neman zaben Gwamna Yahaya Bello da aka yi gabanin zaben da za a yi a jihar a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Cikin sanarwar ta PDP ta fitar ta bakin mai magana da yawunta na kasa, Kola Ologbondiyan, jam'iyyar ta yi ikirarin cewa durkusawa yayin yakin neman zabe alama ce dake nunawa karara cewa "Gwamna Bello ba zai iya samun wani kuri'u ba idan har za ayi zabe na adalci a zaben na ranar 16 ga watan Nuwamba."

DUBA WANNAN: Bidiyon wani almajiri yana Sallah a kan dakalin coci ya dauki hankulan mutane

PDP ta yi martani kan hotun El-Rufai da ya durkusa yana rokon al'umma su yi wa Yahaya Bello afuwa
PDP ta yi martani kan hotun El-Rufai da ya durkusa yana rokon al'umma su yi wa Yahaya Bello afuwa
Source: Twitter

Jam'iyyar ta PDP ta cigaba da cewa, "Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu shima ya durkusa gaban al'umma ya nemi a yafe wa Yahaya Bello wanda hakan na nuna cewa kowa ya san gwamnan bai yi amfani da damar da aka bashi na jagoranci a jihar ba.

"Sai dai ya nemi afuwar ne a kurarren lokaci domin al'ummar Kogi ba za su amince da tubarsa ba bayan ya shafe shekaru hudu yana gana musu azaba.

"Bugu da kari, Yahaya Bello ya nuna wa kowa cewa bai tuba ba duba da yadda bai nuna wata alamar nadama ba yayin da Gwamna El-Rufai da mataimakin gwamnan jihar Edo ke nema masa gafara a gaban al'umma."

PDP ta shawarci Gwamna El-Rufai ya taimakawa Gwamna Bello wurin tsara takardun mika mulki domin zai sha mummunan kaye a zaben da ke tafe a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel