WAEC ta saki sakamakon jarrabawa, ta ce mutane 33,304 cikin 94,884 ne suka lashe darusa 5

WAEC ta saki sakamakon jarrabawa, ta ce mutane 33,304 cikin 94,884 ne suka lashe darusa 5

- Hukumar jarrabawar West African Examination Council (WAEC) ta saki sakamakon jarrabawar Nuwamba/Disamba

- WAEC ta bayyana cewa imlar dalibai 33,304 ne suka yi nasarar lashe darusa biyar ciki harda Lissafi da Ingilishi

- Hukumar ta kara da cewa ta rike sakamakon jarrabawar dalibai 9,457

Rahotanni sun kawo cewa jimlar dalibai 33,304 ne suka yi nasarar lashe darusa biyar ciki harda Lissafi da Ingilishi a jarrabawar WAEC na 2019 a Najeriya.

Hukumar jarrabawar ta WAEC wacce ta saki sakamakon jarraawar a ranar Juma’a, 15 ga watan Nuwamba ce ta bayyana hakan.

Hukumar, ta hannun Olu Adenipekun, Shugaban ofishinta na Najeriya, ta ce ta kuma rike sakamakon jarrabawar dalibai 9,457.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Adenipekun, wanda ya yi Magana a Lagas, ya ce dalibai 94, 884 ne suka yi zaman zana jarrabawar.

Ya ce kaso 35.10% na daliban sun yi nasarar lashe darusa biyar da suka wajaba zuwa sama.

A kamanceceniya, kaso 35. 64% na dalibai ne suka lashe darusa biyar a 2019.

Legit.ng ta rahoto cewa WAEC ta fara sakin sakamakon jarrabawar Mayu/Yuni 2019 a baya inda Adenipekun ya sanar da cewa dalibai 1,596161 ne suka yi rijistan jarrabawar daga sanannun makarantun sakandare 18,639 a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Zaben Bayelsa: Cikakken sunayen yan takarar gwamna, abokan takararsu da kuma jam’iyyunsu

Adenipekun ya kuma bayyana cewa jimlar dalibai 1,020,519 wadanda suka zauna jarrabawar na Mayu/Yuni 2019 sun samu kiredit da sama da haka cikin darusa biyar harda Lissafi da Ingilishi.

A baya mun ji cewa hukumar tsara jarrabawar kammala makarantar sakandire ta kasashen Afrika ta yamma (WAEC) ta amince da nada Mista Pateh Bah a matsayin sabon rijistara da zai yi wa'adin zango daya mai tsawon shekaru biyar.

Mista Bah, dan asalin kasar Gambia, ya fara zangonsa a watan Oktoba kuma ya kare a watan Satumba na shekarar 2024.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel