Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake sace wani Farfesa a Jami'ar Yola

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake sace wani Farfesa a Jami'ar Yola

'Yan bindiga sun sace wani Farfesa a tsangayar nazarin Tsarin Birane na Jami'ar Fasaha ta Modibbo Adama (MAUTECH) dake Yola.

The Nation ta ruwaito cewa a ranar Juma'a cewa an sace Farfesa Felix Ilesani a daren ranar Alhamis a gidansa dake unguwar gidajen ma'aikatan jami'ar dake garin Gire, hedkwatan karamar hukumar Girei na jihar Adamawa.

Farfesan shi ne babban fasto da Trinity Chapel, wani coci dake cikin makarantar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce babban jami'an tsaro na jami'ar ne ya shigar da rahoton.

Ya ce tuni an aike da jami'an 'yan sanda domin bin sahun 'yan bindigan da niyyar ceto farfesan daga hannun wadanda suka sace shi.

DUBA WANNAN: Bidiyon wani almajiri yana Sallah a kan dakalin coci ya dauki hankulan mutane

Felix Ilesani shine Farfesa na biyu na MAUTECH da ya fada hannun masu garkuwa da mutane cikin watanni biyu.

A farkon watan Oktoban ne masu garkuwa da mutane suka sace wani farfesa a tsangayar nazarin kasa mai suna Adamu Zata.

An taba garkuwa da Adamu Zata a baya kafin daga bisani aka sako shi watan Oktoban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel