Zaben Kogi: Tsohon gwamna Dankwambo ya caccaki El-Rufai kan rokarwa Bello gafara

Zaben Kogi: Tsohon gwamna Dankwambo ya caccaki El-Rufai kan rokarwa Bello gafara

- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, bai ji dadin abunda Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ba na rokar wa Yahaya Bello na Kogi gafara akan rashin biyan ma’aikata albashi.

- Dankwambo ya yi al’ajabin yadda za a rokarwa wani gwamna da ke rike da albashin kusan watanni 30 gafara cikin sauki

- Aisha Buhari ma ta roki mutanen jihar Kogi da su gafartawa Bello gabannin zaben ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba

Yan awowi kafin zaben Kogi, wani tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya caccaki Nasir El-Rufai na jihar Kaduna kan rokarwa Yahaya Bello, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gafara.

El-Rufai ya haddasa wani abu mai kama da wasan kwaikwayo lokacin da ya duka kan gwiwowinsa guda biyu a gaban dandazon jama’a da suka hadu a wajen gangamin kamfen din Yahaya Bello domin sauraron alkawaran da zai dauka gabannin zaben.

Hajia Aisha, uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari ma ta roki mutanen Kogi da su yafewa Bello kan albashi da ba a biya su ba.

Da yake martani, Dankwambo wanda ya bar kujerar mulki a Gombe a watan Mayu 2019, ya yi al’ajabin yadda zai yiwu ace an rokarwa gwamnan da ke rike da albashin ma’aikatan jiharsa na kusan watanni 30 gafara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: APC za tayi musharaka a zaben gobe a Bayelsa - INEC

“Ta yaya za ku rokawa wani gwamna da ke rike da albashin ma’aikata na kusan watanni 30 gafara sannan kuma ba zai iya fitowa ya nuna wani aiki guda da ya yi ba tsawon shekaru hudu?” Ya tambaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel