Tashin hankali: Da kaina na tono gawarwakin mahaifana domin na sayar da kasusuwansu

Tashin hankali: Da kaina na tono gawarwakin mahaifana domin na sayar da kasusuwansu

- Jami’an tsaro a kasar Mozambique sun cafke wani mutum a yankin Nampula da ke arewacin kasar

- Laifinsa kuwa shine, zakulo kasusuwan mahaifinsa, mahaifiyarsa da kawunsa don siyarwa

- Mutumin ya amsa laifinsa tare da bayyanawa ‘yan sandan cewa, wani attajirin dan kasuwa ne ya bukaci hakan

Jami’an tsaro a kasar Mozambique sun cafke wani mutum a yankin Nampula da ke arewacin kasar, a kan zarginsa da tono gawarwakin iyayensa da kawunsa don cire kasusuwansu.

Mutumin ya sanar da jami’an tsaron cewa, wani attajirin dan kasuwa ne ya yaudareshi da alkawarin bashi babur da kuma dala 300 kimanin naira dubu dari kenan a kudin Najeriya.

A cewar mutumin, dan kasuwar dai yana harkokin da suka shafi hakar ma’adanai ne a garin Lalaua da ke yankin.

Jami’an tsaron sun cafke mutumin ne a kauyen Ntocol da ke iyakar gundumar Lalaua da Mecuburi.

KU KARANTA: Bidiyo: Wata matsafiya ta rikide ta zama akuya bayan an takurata ta dauki kudin da ta ajiye da gangan dan yara su dauka

Mutumin ya shaidawa BBC cewa: “Dan kasuwar ya bukaci in nemo masa kasusuwan mutanen da suka mutu ba tare da sun yi jinya ba. Idan kuwa nayi hakan, zai bani babur.”

“Babu bata lokaci na garzaya makabartar da ake binne danginmu, na tono kaburburan mahaifina, mahaifiyata da kawuna na ciro kasusuwansu. Na bar Lalaua amma ban yi sa’ar zuwa na samu dan kasuwar ba,” in ji mutumin.

Jami’an ‘yan sanda na tsare da mutumin a ofishinsu da ke yankin Nampula inda ake cigaba da bincike.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan yankin, Zacaria Nacute, ya shaidawa BBC cewa, wannan ne karo na biyar da aka samu irin wannan lamarin a yankin cikin wannan shekarar.

Ana alakanta hakan kuwa da harkoki irin na matsafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel