Yanzu-yanzu: Lauyoyin Atiku sun kaurecewa kotun koli, yayinda ake shirin zayyana dalilan watsi da kararsu

Yanzu-yanzu: Lauyoyin Atiku sun kaurecewa kotun koli, yayinda ake shirin zayyana dalilan watsi da kararsu

Cikin manyan lauyoyi 20 da ke tsayawa jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, babu wanda ya zo kotun koli da safiyar yau Juma'a, 15 ga Nuwamba, da Alkalan kotun ke shirin zayyana dalilansu.

Hakazalika, dukkan kananan lauyoyi PDP da Atiku 30 sun kauracewa kotun kolin yayinda kotu ke shirin kaddamar da zama.

A ranar Laraba, Alkaln kotun koli sun ce zasu bayyana dalilan da yasa sukayi watsi da karar jam'iyyar PDP da Atiku inda suka kalubalanci nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 23 ga Febrairu, 2019.

A bangare guda, lauyoyin shugaba Muhammadu Buhari, jam'iyyar All Progressives Congress APC, da hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC, duk suna hallare a kotun tun misalin karfe 9:05 na safe.

KARANTA: Dan shekara biyar, wasu 1063, sun haddace Al-Kur'ani a Bauchi

Za ku tuna cewa a ranar 30 ga Oktoba, 2019, kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar Atiku Abubakar da PDP amma ta jinkirta bayyana dalilan da yasa ta gabatar da shari'ar.

Kwamitin alkalan kotun bakwai karkashin jagorancin shugaban alkalan Najeriya, Tanko Muhammad, ta tabbatar da nasarar shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyarsa.

Da safen nan, uku daga cikin Alkalan ne suka iso kotun domin karanta hukuncin.

A nashi tsokacin, Atiku Abubakar ya bayyana bacin ransa da takaici kan hukunicn kotun koli da yadda yadda bangaren shari'a, yan jarida, da hukumar zabe ta INEC ba su da karfi a Najeriya.

Atiku ya ce wannan shari'a ya nuna cewa dukkan abinda PDP ta gina a shekaru 16 da tayi mulki na kawo cigaban demokradiyya, wannan gwamnatin ta rusa su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel