Kwastam ta kama jarkokin man fetur 4,500 a Kebbi

Kwastam ta kama jarkokin man fetur 4,500 a Kebbi

- Hukumar Kwastam na Najeriya reshen jihar Kebbi, ta sanar da kama jarkokin man fetur guda 4,500

- Mataimakin kwanturola na hukumar kwastam na Najeriya, Alhaji Bashir Abubakar ne ya bayyana hakan a lolacin wani ziyarar ban girma da ya kaiwa Gwamna Abubakar Bagudu a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba

- Ya ce jami’an kwastam sun kama kayayyakin ne a kauyen Bahindi, karamar hukumar Bagudo da ke jihar

Mataimakin kwanturola na hukumar kwastam na Najeriya, Alhaji Bashir Abubakar ya bayyana cewa hukumar reshen jihar Kebbi ta kama jarkokin man fetur guda 4,500.

Ya ce jami’an kwastam sun kama kayayyakin ne a kauyen Bahindi, karamar hukumar Bagudo da ke jihar.

Abubakar, wanda ke kula shirin rufe iyakoki na sashi na 4 ya bayyana haka a lolacin wani ziyarar ban girma da ya kaiwa Gwamna Abubakar Bagudu a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba.

Ya ce: “An lura cewa gidajen man fetur da dama a yankunan iyakar kasar na samun man fetur, amma basa siyarwa da mutane. Sun gwammaci yin fasa kaurinsa zuwa wajen kasar.”

Ya ce tawagarsa sun kasance hadi na jami’an tsaro da aka hada domin kare rayuka, dukiyoyi da tattalin arzikin kasar sannan cewa saboda halin rashin tsaro, akwai bukatar kula da iyakokin kasar.

Ya ce rahoton tsaro ya nuna ana shigo da makamai da alburusai da kuma shigowar mutane kasar ba bisa ka’ida ba.

KU KARANTA KUMA: Pantami ya yi umurnin dakatar da sakon voicemail kai tsaye a layukan waya

Mataimakin Gwamnan, Alhaji Samila Dabai, wanda ya tarbe shi a madadin gwamnan, ya yaba da kokarin jami’an sannan ya jinjinawa matakan da gwamnatin tarayya ta dauka domin kare iyakokin kasar.

Ya ce jihar Kebbi ta amfana daga matakan gwamnatin tarayya saboda jihar na raba iyaka da Nijar da kasar Benin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel