Yanzu-yanzu: Dan shekara biyar, wasu 1063, sun haddace Al-Kur'ani a Bauchi

Yanzu-yanzu: Dan shekara biyar, wasu 1063, sun haddace Al-Kur'ani a Bauchi

Dan shekara biyar da haihuwa, Mubashshiru Sheikh Dahiru Bauchi , da wasu dalibai 1063, sun kammala haddadar Al-Kurani mai girma a jihar Bauchi, Arewa maso gabashin Najeriya.

Mahaddatan na cikin dalibai 1501 da aka yaye a makarantu 300 na shahrarren malamai, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

A taron yaye daliban da ya gudana a farfajiyar filin kwallon kafar Abubakar Tafawa Balewa, Sheik Dahiru Bauchi, ya ce daliban sun zo ne daga jihohin Bauchi, Kano, Katsina, Kaduna, Kwara, Adamawa, Borno da Niger.

Ya kara da cewa a cikin dalibai 1500, guda 1064 sun haddace Al-kur'ani gaba dayanta yayinda 437 suka koyi karatun Al-Kur'ani.

Ya yi kira ga daliban suyi amfani da ilimin da suka samu wajen yada addinin Musulunci.

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir, ya ce gwamnatinsa za ta bada gudunmuwar kudade ga makarantun addini domin gyara tarbiyyan al'umma.

Ya ce za'a sanya dukkan Islamiyyoyin jihar cikin shirin gyare-gyare da gine-ginen makarantun gwamnatin jihar.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel