‘Yan siyasa su na tura ‘Ya ‘yansu karatu, su maida sauran yara karnukan siyasa – Jonathan

‘Yan siyasa su na tura ‘Ya ‘yansu karatu, su maida sauran yara karnukan siyasa – Jonathan

A Ranar 14 ga Watan Nuwamba, 2019, tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, ya yi wani bayani game da tsarin zabe a lokacin kaddamar da wani littafi da aka yi a Garin Fatakwal.

Tsohon shugaban kasar ya zargi ‘yan siyasa da laifin horas da yara da ake amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa. Jaridar The Nation ta rahoto wannan a jiya daga babban birnin jihar Ribas.

Goodluck Jonathan ya ke cewa yayin da ‘Yan siyasa su ke tura ‘Ya ‘yansu na cikinsu zuwa manyan jami’o’in Duniya domin su yi karatu, su na amfani da yaran mutane wajen yin bangar siyasa.

Dr. Jonathan ya ke cewa da yara ake amfani wajen kawo matsalolin zabe a kasar. Tsohon shugaban kasar ya ba kuma bada shawarar yadda za a kawo karshen magudin siyasar da ake tafkawa.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban INEC ya bada shawarar hanyar gyara zabe a Najeriya

A cewar tsohon shugaban na Najeriya, tsarin zabe da na’urorin zamani shi ne zai kawo karshen murdiyar zabe da aka yi. Jonathan ya ce idan ba haka ba, bata-gari za su cigaba da rike mulki.

Ga jawabin tsohon Shugaban: “Ganin abubuwan da su ke faruwa yanzu, an shiga lokacin zabe a jihohin Bayelsa da Kogi. Abubuwan da mu ke gani a jihohin nan biyu su na da ban takaici.”

“Tuni an fara harbe-harbe, ana amfani da ‘yan dabar siyasa, har an kashe wasu, a yayin da ba a kai ga fara ainihin zaben ba ma tukuna. Ba a bukatar a kai lokacin da katin zabe bai da amfani.

Jonathan wanda ya yi mulki daga 2010 zuwa 2015 a Najeriya ya yi kira ga Najeriya da sauran kasashe masu tasowa su rungumi zabe ta hanyar amfani da na’ura domin a rage yawan magudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel