Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon ministan labaran Najeriya rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa tsohon ministan labaran Najeriya rasuwa

- Tsohon ministan labarai na Najeriya, Cif Alex Akinyele ya rasu a daren ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba a jihar Ondo

- Daya daga cikin yaran Akinyele, Constantine Akinfolarin Akinyele, ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa

- Tsohon ministan ya taba rike mukamin cibiyar hulda da jama’a na Najeriya wato Nigerian Institute of Public Relations (NIPR)

Allah ya yiwa tsohon ministan labarai na Najeriya, Cif Alex Akinyele rasuwa.

A wani jawabi daga daya daga cikin yaransa, Constantine Akinfolarin Akinyele, ya tabbatar da cewa jigon na Ondo ya rasu a daren ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba, bayan dan gajeren rashin lafiya.

Akinyele, wanda ya kasance kwararren jami’in hulda da jama’a, bayan aiki a matsayin ministan labarai, ya kuma riki makamin shugaban kungiyar wasanni na Najeriya.

Ya kuma kasance tsohon shugaban cibiyar hulda da jama’a na Najeriya wato Nigerian Institute of Public Relations (NIPR).

KU KARANTA KUMA: Pantami ya yi umurnin dakatar da sakon voicemail kai tsaye a layukan waya

A wani labari na daban, mun ji cewa wata dagacin kauyen Ikot Uduak, da ke cikin karamar hukumar Calabar a jihar Cross River ta fada kabarin wasu ma'aurata a kauyen don hana a binne su.

Kamar yadda Daily Post ta ruwaito, dagacin kauye, mai martaba Efio-Awan Asuqo Asibon ta ce, ba za a binne ma'auratan masu suna Mr da Mrs Ekpe Okon Edet a kauyen ba saboda ba asalin 'yan garin bane.

Basset Okon Edet, daya daga cikin 'ya'yan ma'auratan da suka rasu, yayin bada bayanin lamarin, yace, "wannan gawarwakin iyayena ne kuma gidan nan kakana ne ya siya. Mahaifina Ekpe Okon Effiom ya ci gado. Muna da takardun yarjejeniyar filin."

Dagacin kauyen Efio-Awan Asibong, kamar yadda rahoto ya sanar tace 'yan hayanta ne. Tayi bayanin cewa basu da takardun shaidar mallakar wajen. Ta yi alakwarin in har aka birne gawarwakin sai ta sa an konesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel