Inganta tsaro: Babban sufetan Yansanda ya nada sabbin kwamishinoni a jahohi 7

Inganta tsaro: Babban sufetan Yansanda ya nada sabbin kwamishinoni a jahohi 7

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu ya aika da sabbin kwamishinonin Yansanda zuwa wasu jahohin Najeriya guda 7 domin samar da ingantaccen tsaro a cikin jahohin da kewayensu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito babban sufetan ya dauki wannan mataki ne biyo bayan karin girma da wasu kwamishinonin Yansanda suka samu zuwa mukamin mataiman sufetan Yansanda, watau AIG.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya dauke Yansandan dake gadin gwamnonin Kogi da Bayelsa

Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Frank Mba ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, inda yace nadin mukaman ya fara aikin nan take ne, sa’annan ya zayyana sunayen sabbin kwamishinonin da jahohinsu kamar haka;

Habu Sani Ahmadu jahar Kano, Lawal Jimeta jahar Edo, Phillip Sule Maku jahar Bauchi, Nkereuwem A Akpan jahar Cross Rivers, Kenneth Ebrimson jahar Akwa Ibom, Odumusu Olusegun jahar Legas da Imohimi Edgal jahar Ogun.

Babban sufetan ya yi kira ga sabbin kwamishinonin da su tabbata sun daura daga inga magabatansu suka tsaya musamman wajen samar da tabbataccen tsaro a jahohin da aka turasu su yi aiki, sa’annan ya yi kira a garesu dasu yi aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki a jahohin don cimma manufa.

Daga karshe babban sufetan Yansandan ya nemi al’ummar jahohin guda bakwai su baiwa sabbin kwamishinonin hadin kai tare da goyon baya domin tabbatar da tsaro tare da kare dukiya da rayukansu.

A wani labarin kuma, yayin da ake shirye shiryen shiga zaben gwamna a jahohin Kogi da Bayelsa a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Abubakar Adamu ya janye dukkanin jami’an Yansandan dake gadin gwamnonin jahohin biyu.

IG ya dauke Yansandan dake gadin Gwamna Yahaya Bello na Kogi da Gwamna Seriake Dickson na Bayelsa, da na mataimakansu, kwamishinoni da duk wasu masu rike da mukaman siyasa a jahar.

Mataimakin babban sufetan Yansanda, DIG Abdulmajid Ali ne ya bayyana haka a garin Lokoja yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis game da shirye shiryen da rundunar Yansandan Najeriya take yi a kan zabukan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel