Zamfara: Matawalle ya ragewa manyan sakatarorin gwamnati 19 matsayi, ya bayyana dalili

Zamfara: Matawalle ya ragewa manyan sakatarorin gwamnati 19 matsayi, ya bayyana dalili

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Marawalle ya kirkiri sabbin ma'aikatu na Tsaro da Ayyukan cikin gida a yayin da ya rage adadin sakatarorin dindindin a jihar daga 46 zuwa 27.

Gwamnan ya bayar da wannan sanarwar ce a wata jawabin da ya yi a daren ranar Alhamis inda ya ce an dauki wannan matakin ne domin inganta ayyuka a jihar.

A cewar gwamnan, wadanda ba su yi nasarar cin jarabbawar ba za a rage musu mukami kuma a mayar da su sakatarori da direktocin wasu hukumomi.

Gwamna Matawalle ya bayyana sunayen sabbin ma'aikatan da aka kirkira kamar haka; Ma'aikatan Harkokin Filaye, Gidaje da Cigban birane, Ma'iakatan harkokin sarauta, Ma'aikatan ayyukan jin kai, Ma'aikatan inganta alaka tsakanin al'umma, da kuma ta Ayyukan al'umma.

DUBA WANNAN: Bidiyon wani almajiri yana Sallah a kan dakalin coci ya dauki hankulan mutane

Gwamnan ya ce, "Gwamnati ta rage adadin sakatarorin dindindin daga 46 zuwa 27. Anyi hakan ne bayan an shirya wa sakatarorin jarrabawa ta rubutu da ta baka."

Gwamnan ya cigaba da cewa anyi wannan canje-canjen ne sakamakon rahoton da wata kwamiti na musamman da aka kafa don gano hanyoyin da za a inganta ayyuka a jihar ta bayar.

Gwamna Matawalle ya bawa al'ummar jihar tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da nemo hanyoyin inganta ayyukan gwamnati don kawo cigaba da rayuwar al'umma da ayyukan gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel