Babban sufetan Yansanda ya dauke Yansandan dake gadin gwamnonin Kogi da Bayelsa

Babban sufetan Yansanda ya dauke Yansandan dake gadin gwamnonin Kogi da Bayelsa

Yayin da ake shirye shiryen shiga zaben gwamna a jahohin Kogi da Bayelsa a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Abubakar Adamu ya janye dukkanin jami’an Yansandan dake gadin gwamnonin jahohin biyu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito IG ya dauke Yansandan dake gadin Gwamna Yahaya Bello na Kogi da Gwamna Seriake Dickson na Bayelsa, da na mataimakansu, kwamishinoni da duk wasu masu rike da mukaman siyasa a jahar.

KU KARANTA: Kasashen Najeriya, Nijar da Kwatano sun kafa kwamitin tattaunawa game da kulle iyakoki

Mataimakin babban sufetan Yansanda, DIG Abdulmajid Ali ne ya bayyana haka a garin Lokoja yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis game da shirye shiryen da rundunar Yansandan Najeriya take yi a kan zabukan.

DIG Ali yace rundunar Yansanda za ta janye jami’anta dake tsaron gwamnonin da sauran rukunin mutanen da umarnin ya shafa har sai bayan kammala zabukan. Sa’annan yace rundunar ta tanaji isashshen tsaro a jahohin biyu ta yadda za’a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

DIG Ali ya cigaba da cewa sun tura jami’an Yansanda 66,241 zuwa jahohin Bayelsa da Kogi domin su kula da zabukan da za’a gudanar tare da tabbatar da tsaro a jahohin biyu.

Daga karshe yace suna sane da kokarin tayar da hankula da wasu mutane ke shirin yi a yayin zabukan, don haka yace suna gargadinsu cewa ba zasu lamunta duk wani take takensu na tayar da zauni tsaye ba.

“Ba zamu yi kasa a gwiwa wajen bankado duk masu riin wannan manufa ba, za mu kamasu, tare da tabbatar an hukuntasu kamar yadda doka ta tanada” Inji shi.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, kuma tsohon shugaban jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa inganci da sahihancin zabe shi ne jigon cigaban dimukradiyya a kowacce kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel