Attahiru Jega ya bada shawara game da inganta ingancin zabe a Najeriya

Attahiru Jega ya bada shawara game da inganta ingancin zabe a Najeriya

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, kuma tsohon shugaban jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa inganci da sahihancin zabe shi ne jigon cigaban dimukradiyya a kowacce kasa.

Jega ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da kasida a kan rawar da jami’o’I zasu taka wajen samar da shihiyar zabe a Najeriya, a jami’ar Ibadan , inda yace akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA: Kasashen Najeriya, Nijar da Kwatano sun kafa kwamitin tattaunawa game da kulle iyakoki

“An tabbatar da kare dimukradiyya na daga cikin abubuwan da zasu iya tabbatar da cigaba mai daurewa, amma akwai abinda bamu lura da shi, kuma shine samar da ingantaccen zabe shi ne hanya kadai na tabbatar da cigaban da dimukradiyya.

“Gudanar da sahihin zabe shi ne hanyar cigaban dimukradiyya a Najeriya da dukkanin kasashen nahiyar Afirka dake fama da matsalolin shugabanci. Zabuka a Najeriya na tattare da matsaloli daban daban tun daga shirin kafin zabe, yayin zabe da kuma bayan zabe.

“Dole ne dukkanin masu ruwa da tsaki su aiki tare domin shawo kan wannan matsala.” Kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shi.

Jega ya yaba da rawar da jami’a da malaman jami’a ke takawa wajen kara ma zabukan Najeriya inganci tun daga shekarar 2011, don haka ya nemi su kara kaimi wajen gudunmuwar da suke bayarwa ta hanyar gudanar da bincike wajen samar da kayayyakin zabe a cikin gida.

Sai dai Jega ya bayyana wasu fannonin zabe a Najeriya dake bukatar a kellesu da idon basira domin a basu kulawar da ta dace tare da ciyar dasu gaba, da suka hada da; bangaren dokokin sharia, amfani da kimiyya da fasaha da kuma yin abubuwa a bayyane kowa ya gani.

A nasa jawabin, shugaban jami’ar Ibadan, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Idowu Olayinka ya bayyana cewa akwai bukatar duk dan Najeriya ya damu da tsaftace zabukan kasar domin gudanar da zaben gaskiya da gaskiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel