Bidiyo: Yadda aka kama wasu matasa guda hudu suna yiwa wata yarinya fyade ta karfin tsiya

Bidiyo: Yadda aka kama wasu matasa guda hudu suna yiwa wata yarinya fyade ta karfin tsiya

- Bidiyon wasu yara maza hudu da suka yi wa wata yarinya fyade ya baza kafafen sada zumunta

- Duk da ba a san ta yadda aka yi aka dau bidiyon ba, an ga wani yaro na kalubalantar mummunar dabi'ar a bidiyon

- A bidiyon, an ga yarinyar na kokarin kwatar kanta, amma yaran maza sun yi amfani da karfinsu inda suka dinga lalata da ita, daya bayan daya

Bidiyon wasu yara guda hudu da suka yi wa wata yarinya fyade, daya bayan daya ya bazu a shafukan sadarwa na zamani.

Duk da dai ba a san yadda aka yi har aka dau bidiyon ba, yanzu haka bidiyon ya bazu ko ina a shafukan sada zumunta inda yake ta jawo kace-nace.

Ba a san ta yadda aka dauki wannan bidiyon ba amma kuma ya gama gari.

A cikin bidiyon an nuno yarinyar ta na kokarin kwatar kanta daga wajen yaran maza guda hudu amma da yake sun fi karfinta babu yadda ta iya hada ta hakura.

Dama kuma, ba a hada karfin mace da namiji, koda kuwa shekarunsu daya.

KU KARANTA: To fah: Fasto ya ciyar da mabiyanshi masu neman karama da tsutsotsi a cikin coci

Hakan yasa wasu mugayen mazan masu mummunar dabi'a su kan yi amfani da wannan banbancin na karfi da Allah ya ba su wajen yiwa mata fyade babu gaira babu dalili.

Har ya zuwa yanzu dai a kasar nan babu tabbataccen hukunci kwakkwara ga mazan da aka kama da laifin fyade. Hakan ne ya sanya duk ranar duniya mummunar dabi'ar fyade ke aukuwa a Najeriya.

Bayan tozarci da cin mutunci da ke kunshe da fyade, akan sanya wa matan damuwa mai yawan gaske a cikin zuciyar su wacce a lokuta da dama kan kai su ga halaka kan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel