Kasashen Najeriya, Nijar da Kwatano sun kafa kwamitin tattaunawa game da kulle iyakoki

Kasashen Najeriya, Nijar da Kwatano sun kafa kwamitin tattaunawa game da kulle iyakoki

Gwamnatin kasar Najeriya, Nijar da Bini sun kafa kwamitin hadaka domin tattauna game da rufe iyakoki da Najeriya ta yi, tare da kokarin lalubo hanyar shawo kan matsalar, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kasashen uku sun kafa kwamitin hadaka daya kunshi Yansanda, hukumar yaki da fasa kauri da kuma hukumar kula da shige da fice na kasashen uku domin su gudanar da sintiri a kan iyakokin kasashen.

KU KARANTA: Jami’an NDLEA sun yi ram da wani gagararren dillalin miyagun kwayoyi a Imo

Kasashen sun amince da kafa wannan kwamiti ne bayan zaman tattaunawa da suka da juna a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, inda ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa kasashen sun lura da dukkanin korafe korafen da kowannensu ya gabatar.

Ministan yace kwamitin zai hada da ministocin kudi, cinikayya da kasuwanci, harkokin kasashen waje, kwastam, hukumar shige da fice da kuma ofishin mashawartan shuwagabannin kasashen uku a kan lamurran tsaro.

Ministan ya kara da cewa babban aikin kwamitin shi ne tabbatar da sun dauki matakan haramta safarar mutane da fasa kaurin kayayyaki zuwa kasashen uku ba tare da ka’aida ba, haka zalika kwamitin za ta habbaka cinikayyar kasuwanci tsakanin kasashen uku.

Bugu da kari kwamitin za ta samar da hukunce hukuncen da suka kamata kowacce kasa ta dauka game da kayayyakin da aka yi fasa kaurinsu.

Minista Onyeama ya kara da cewa: “Gwamnatocin kasashen uku sun amince da matakin kyale duk wani mutumin da zai shiga cikinsu kuma yana dauke da fasfon na kungiyar kasashen nahiyar Afirka, ECOWAS, amma ta hanyoyin da aka kayyade.

“Akwai kwamitin tsaro da zasu gudanar da sintiri a iyakokin kasashen uku, kuma ta kunshi Yansanda, hukumar yaki da fasa kauri da kuma hukumar kula da shige da fice na kasashen uku, wanda za ta yi zamanta na farko a ranar 25 zuwa 27 ga watan Nuwamba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel