An kaurace wa aure a wani gari a Kano bayan maigari ya wajabta biyan harajin biki

An kaurace wa aure a wani gari a Kano bayan maigari ya wajabta biyan harajin biki

Mazauna wani kauye a jihar Kano sun kaurace wa aure domin nuna rashin amincewarsu ga wani haraji da mai garinsu ya kirkiro.

BBC ta ruwaito cewa, an shafe tsawon watanni hudu a kauyen, babu wanda ya yi aure bayan da mai garin ya saka harajin.

Harajin da mai garin ya kirkiro ya maye gurbin al'adar yin kayan lefe da maza ke yi wa 'yan matan da zasu aura.

Mai garin, Ali Saad, ya ce sabon harajin ya fi sauki, amma kuma, sai ga shi ya jawo fushin samari, lamarin da yasa suka kaurace wa aure na tsawon watanni hudu.

DUBA WANNAN: APC: Kotun daukaka kara ta sake kwace kujerar mamba a majalisar wakilai daga Bauchi

A wani cigaba kuma, dagacin garin Kera da ke karamar hukumar Garko ta jihar Kano, ya saka dokar kayyade kudin aure da sadaki a garin. Kamar yadda dagacin ya sanar, budurwa kudin aurenta da sadaki su tsaya a N137,000 inda bazawara kuma a dinga biyan N50,000.

Kusan watanni uku kenan da dagacin, dattijon arziki, Malam Bello Musa ya kafa wannan dokar. Amma sai dai iyaye sun nuna tsananin damuwarsu tare da kokawa kan wannan sabon cigaban.

A tattaunawar da gidan rediyon Freedom na Kano yayi da wasu iyayen yara a garin, sun nuna ko kadan ba zasu lamunci wannan sabon tsarin ba. A don haka ne suka shiryA tsaf don kai kokensu gaban hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel