Yanzu-yanzu: An nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas

Yanzu-yanzu: An nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas

An nada sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Legas mai suna CP Hakeem Olusegun Odumosu kamar yadda Tvc news ta ruwaito.

CP Hakeem zai maye gurbin mataimakin sufeta janar na 'yan sanda, AIG Zubairu Muazu da ka yi wa karin girma cikin 'yan kwanakin nan da ya kasance kan kujerar tun bayan CP Edgal Imohimi.

Idan ba a manta ba hukumar kula da walwalar 'yan sanda PSC a baya-bayan nan ta yi wa kwamishinonin 'yan sanda bakwai karin girma zuwa mukamin AIG.

Yanzu-yanzu: An nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas

Yanzu-yanzu: An nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas
Source: Twitter

Cikinsu akwai CP Zubairu na Legas, Danmallam Muhammed na jihar Edo fa Ahmed Iliyasu na jihar Kano.

Hakeem Odumosu ya taba rike mukamin shugaban Hukumar Kula da Muhalli ta Legas a zamanin mulkin Gwamna Ahmed Bola Tinubu.

DUBA WANNAN: 'APC' ta dakatar da Gwamna Obaseki da mataimakinsa a kan zargin za su koma PDP

Daga bisani ya kuma rike mukamin babban kwamandan 'yan sandan RRS a zamanin mulkin Gwamna Raji Babatunde Fashola a jihar ta Legas.

Daga nan kuma an masa karin girma zuwa kwamishinan 'yan sanda ACP kuma ya koma garin Akwanga a jihar Nasarawa a matsayin Area Kwamanda har lokacin da ya samu matsayin kwamishinan 'yan sanda wato CP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel