Yanzu-yanzu: Bayan makonni biyu, an kubuto da Alkalin kotun afil da aka sace

Yanzu-yanzu: Bayan makonni biyu, an kubuto da Alkalin kotun afil da aka sace

Alkalin kotun daukaka kara da ke Benin, jihar Edo, Justice Chioma Nwosu-Iheme, ta samu kubutowa bayan makonni biyu a hannun masu garkuwa da mutane da suka sace ta.

Kwamishanan yan sandan jihar Edo, Danmallam Mohammed, ya tabbatar da hakan ne inda yace an kubuto da Alkalin kuma tana wajen iyalanta.

Garkuwa da Alkalin ya fusata lauyoyin jihar inda suka kauracewa kotun na tsawon kwanaki uku a makon da ya gabata.

Yanzu-yanzu: Bayan makonni biyu, an kubuto da Alkalin kotun afil da aka sace

Justice Chioma Nwosu-Iheme
Source: UGC

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun barranta kansu daga kira ga Oshiomole yayi murabus

Mun kawo muku rahoton cewa an yi garkuwa da wata Alkalin kotun Najeriya, shiyar Benin, Chioma Nwosu, da safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2019 a hanayar Benin-Agbor, jihar Edo.

An kashe dan sanda dogarinta a wajen.

Hakazalika A ranar 25 ga Oktoba, masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Alkalin babban kotun tarayya dake Akure, birnin jihar Ondo, Justice Abdul Dogo.

An sace Alkali Abdul Dogo a ranar Talata yayinda yake hanyar komawa garin Akure daga birnin tarayya Abuja.

An samu rahoton cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Alkalin kuma sun bukaci N50 million kudin fansa.

Amma bayan kwana daya, sun sako shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel