Aisha Buhari ta fadi abinda ya hana Gwamna Bello biyan albashi a watannin a baya

Aisha Buhari ta fadi abinda ya hana Gwamna Bello biyan albashi a watannin a baya

First Lady, Aisha Buhari ta ce aikin tantance ma'aikatan gwamnati a jihar Kogi ne dalilin da yasa Gwwamna Yahaya Bello ya kasa biyan albashi a jiharsa.

Matar shugaban kasar ta ce tun bayan kammala aikin tantancewar, ma'aikatan jihar sun fara samun albashinsu a kan lokaci kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Hakan yasa Aisha Buhari ta roki al'ummar jihar su yi wa Bello afuwa kan halin da suka shiga na matsi yayin aikin tantancewar inda ta roki su manta wahalhalun da suka sha a baya.

Aisha ta yi wannan jawabin ne a taron yakin neman zabe na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis jim kadan bayan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya durkusa gaban al'ummar ya roki su yafe wa gwamnan.

A yayin da ta ke jawabi ga mahalarta taron, Aisha Buhari ta ce, "Kamar yadda gwamnan jihar Kaduna ya durkusa ya roke ku nima ina so in ce al'umma su yafe abinda ya faru a baya su manta da shi.

DUBA WANNAN: 'APC' ta dakatar da Gwamna Obaseki da mataimakinsa a kan zargin za su koma PDP

"Kamar yadda aka sani, miji na ya saba magana a kan albashi. An dauki lokaci mai tsawo kafin aka tantance ma'aikatan Kogi sannan aka warware matsalar albashin.

"Amma wannan karon, ku zabe shi domin ya cigaba da biyan albahsi a kan lokaci."

Aisha Buhari ta kuma gayyaci gwamnan zuwa mimbari tana mai cewa, "Ina son Yahaya Bello ya yi muku jawabi kan biyan albashi a kan lokaci."

A jawabin da ya yi, gwamnan ya ce, "Mun fara biyan albashi a kan lokaci." Ma'aikatan jihar za su iya min shaida.

"Mai girma, kin bayar da umurni, kin bamu goyon baya kuma mun biya albashi da ariyas kuma za mu cigaba da biyan albashi a kan lokaci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel