Gwamnonin APC sun barranta kansu daga kira ga Oshiomole yayi murabus

Gwamnonin APC sun barranta kansu daga kira ga Oshiomole yayi murabus

Gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun barranta kansu daga kiran dirakta janar na kungiyar gwamnonin, Salihu Lukman, inda ya ce shugaban jam'iyyar APC yayi murabus.

A ranar Laraba, Saliu Lukman ya yi kira ga Kwamred Adams Oshiomole ya shirya taron shugabannin uwar jam'iyyar ko ya yi murabus.

Majiya mai karfi daga gwamnonin ya ce ba zai yiwu gwamnonin APC suyi irin wannan kira ba.

Majiyan yace: "Dirakta janar aikin gabansa yakeyi kawai."

Hakazalika an samu labarin cewa babu wata ganawa da gwamnonin APC sukayi da suka tattauna lamarin dake wakana da zai sa suyi irin wannan furuci da diraktan kungiyar ya sanar.

DUBA NAN Kotun daukaka kara ta hana aiwatar da shari'ar hana APC takara a Bayelsa

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC ta kasa (shiyar kudu), Hillard Esa, ya yi watsi da kalaman Lukaman inda yace dirakta janar din aikin kansa yakeyi, babu wanda ya sa shi.

Kakakin kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC a jihar Ogun, Mista Tunde Oladunjoye, ya ce gwamnan jihar, Dapo Abiodun, bai san da wannan magana ba.

Yace: "Ina da tabbacin cewa gwamnanmu, Prince Dapo Abiodun, bai da hannu cikin wannan abu kuma ba zai yiwu ya sa hannu ba."

"Bayan sanannen abu cewa gwamnonin basu zauna suka tattauna hakan ba, akwai dokokin da hanyoyin kiran ganawar shugaban koli na jam'iyya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel