APC: Kotun daukaka kara ta sake kwace kujerar mamba a majalisar wakilai daga Bauchi

APC: Kotun daukaka kara ta sake kwace kujerar mamba a majalisar wakilai daga Bauchi

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Jos, jihar Filato, ta soke zaben Honarabul Tata Umar, mamba a majalisar wakilai daga mazabar Zaki ta jihar Bauchi.

Kotun ta yanke hukuncin ranar Alhamis, sannan ta bawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) umarnin sake gudanar da sabon zabe.

Honarabul Umar ne ya daukaka kara zuwa kotun, bayan kotun sauraron korafin zabe ta zartar da hukuncin soke zabensa.

A cikin hukuncin da babban alkalin kotun, Jastis Moses Ugor, ya karanta, yace kotun daukaka karar ta amince da hukuncin da kotun farko ta zartar.

DUBA WANNAN: An tura dan majalisa gidan yari saboda dukan wata mata

A cewarsa, kotun sauraron korafin zabe ta yanke hukuncin da ya dace, wato bayar da umarnin sake gudanar da zabe a wasu mazabu guda uku da ke karamar hukumar Zaki.

Tun a hukuncin farko, kotu ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, da ta kwace shahadar cin zabe da ta ba wa Honarabul Umar.

Kotun daukaka karar ta ce, ta yi watsi da bukatar Honarabul Umar ne saboda rashin gamsuwa da hujjojin da ya dogara dasu.

Ba yanzu aka fara lamarin ta leko, ta koma ga 'yan siyasar ba. So da yawa na kwace kujerun wasu na ba wa abokan adawarsu, ind wasu kuwa ke nasarar cin galaba a tabbatar musu da nasararsu a kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel