Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tsagaita aiwatar da shari'ar hana APC takara a Bayelsa

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tsagaita aiwatar da shari'ar hana APC takara a Bayelsa

Kotun daukaka kara dake birnin tarayya Abuja ta tsagaita aiwatar da shari'ar babban kotun tarayya da ta haramtawa jam'iyyar musharaka cikin zaben daza'a gudanar ranar Asabar.

Karamin ministan man fetur, Cif Temipre Sylva, ya bayyana hakan da yammacin nan a Abuja.

Ministan yayinda yake hira a tashar Channels TV cewa gurbatattun alkalai ne suke son amfani da barakar da ke cikin jam'iyyar wajen kokarin hana jam'iyyar takara gaba daya.

A jiya, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da APC daga gabatar da dan takarar gwamna a jihar Bayelsa.

A cikin hukuncin da kotun, a karakashin mai shari'a, Jastis I. E Ekwo, ta yanke, ta ce ta haramta wa jam'iyyar APC da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tsayar da 'yan takarar gwamna da mataimaki a zaben ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Kotun ta zartar da hukuncin ne biyo bayan karar da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, da mataimakinsa, Sanata Lawarence, Ewhruojakpo, suka shigar a gabanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel