Kogi 2019: El-Rufai ya durkusawa jama'ar jihar Kogi don nemawa Yahaya Bello afuwa

Kogi 2019: El-Rufai ya durkusawa jama'ar jihar Kogi don nemawa Yahaya Bello afuwa

A ranar Alhamis ne, Gwamna Nasir el- Rufai na jihar Kaduna, ya durkusa gaban mutanen jihar Kogi, tare da rokonsu yafiya ga Gwamna Yahaya Bello akan laifukansa garesu.

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, shima ya durkusa ma jama'ar tare da el-Rufai. Amma kuma, Yahaya Bello bai bi ayarin ba.

A yayin jawabi ga jama'ar jam'iyyar APC a Lokoja, el-Rufai yace, da yarinta tattare da Bello lokacin da ya zama gwamna kuma hakan ne yasa ya tafka kura-kurai.

Gwamnan jihar Kadunan yace, tuni gwamnan ya gyara kura-kurensa.

Ya ce, "Mutane da yawa sun ce Yahaya Bello yaro ne; ya yi fada da mutane da yawa. Duk wanda gwamnan ya bata wa, ina rokar masa yafiya. Yaro ne; akwai yuwuwar yayi kura-kurai. Idan yarinta na dibar mutum, yana iya yin kura-kurai amma kana koyo darussa daga hakan,"

DUBA WANNAN: Dadin kowa: Kamaye ya bayyana dalilin da yasa yake fitowa talaka tilis

"A madadinsa, ina durkushe gaban ku, ina rokon masa yafiya idan ya saba muku. Ya damu da mutanen jihar Kogi. Ya damu da jihar baki daya. Ya kawo cigaba ga jihar; ya inganta rayukan matasa da mata a gwamnatinsa," cewar gwamnan Kadunan.

"Ya biya albashin da ya gada daga gwamnatin da ta gabata. Yakamata ku goyi bayansa. Ina rokonku, komai ya zama tarihi. Marigayi Prince Audu yayi duk abinda zai kawo cigaba ga jihar nan. Kada mu tozartasa ta hanyar barin PDP ta samu matsuguni a gidan Lugard." In ji shi.

Ya ce, jam'iyyar PDP bata tsinana komai ba a jihar lokacin da ta yi mulkin shekaru 13 a jihar. A don haka yake kira da a maida jam'iyyar adawar gawa.

El-Rufai ya kara da cewa, "A shekaru 4 da Gwamna Yahaya Bello ya yi a mulkin jihar, ya kawo cigaban da PDP bata kawo ba a shekaru 13 da ta yi a mulkin jihar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel