Yanzu -Yanzu: Kotu ta aminta da takarar APC a zaben gwamnan jihar Bayelsa

Yanzu -Yanzu: Kotu ta aminta da takarar APC a zaben gwamnan jihar Bayelsa

Kotun daukaka kara dake Fatakwal, jihar Rivers, ta aminta da dakatar da hukuncin babbar kotun tarayya dake Yenagoa. Kotun tarayyar ta dakatar da dan takarar jam'iyyar APC ne daga shiga zaben jihar da za a yi a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, kamar yadda jaridar Independent Nigeria ta ruwaito.

Amma Kotun daukaka karar ta bawa dan takarar gwamna na jam'iyyar ta APC ikon shiga zaben a dama da shi.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta ce ba za a fasa yin zaben ranar Asabar din ba duk da hukuncin da kotu ta yanke.

DUBA WANNAN: 'APC' ta dakatar da Gwamna Obaseki da mataimakinsa a kan zargin za su koma PDP

Ta ce duk da haka za ta yi biyaya da hukuncin da kotun ta yanke kan zaben.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe, Mista Festus Okoye ne ya shaidawa The Nation a hirar wayar tarho a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce tuni an samar da dukkan kayayyakin zabe zuwa wuraren da ya dace inda ya ce za a gudanar da zaben a ranar Asabar kamar yadda aka tsara tun farko.

Ku cigaba da bibiyar mu don samun cikakken rahoton ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel