Jama’a sun yi ca a kan Majalisar Dattawa saboda yunkurin kawo wata doka

Jama’a sun yi ca a kan Majalisar Dattawa saboda yunkurin kawo wata doka

Majalisar Dattawa ta kawo wani kudiri da zai sa a kafa wata hukuma guda ta musamman domin yakar masu yin kalamai na batanci ko kiyayya da ka yi jawo zaune tsaye a fadin Najeriya.

Aliyu Sabi Abdullahi shi ne ya kawo wannan kudiri mai suna “National Commission for the Prohibition of Hate Speech (Estb. etc) Bill na shekarar 2019 wanda aka karanta a zauren majalisar.

Jama’a da-dama da kungiyoyi sun fito su na sukar wannan kudiri na Sanata Aliyu Sabi Abdullahi. Daga cikin wadanda su ka nuna rashin goyon bayansu har da Jagoran adawa, Atiku Abubakar.

Sanatan na jihar Neja ya taba kawo irin wannan kudiri a majalisar Bukola Saraki. Kudirin bai iya zarcewa mataki na biyu ba aka yi waje da shi daga majalisar saboda rashin karbuwa da ya samu.

Kudirin ya nemi a bada damar yankewa wanda ya fito ya yi kalamai na kiyayya hukuncin daurin shekaru goma, ko kuma ya biya tara, har ma za ta iya sa a kashe shi har lahira ta hanyar rataya.

Dokar za ta yi aiki a kan duk wanda ya yi amfani ko ya wallafa, ko gabatar ko ya yada wani abu mai kunshe da kalaman da ke iya jawo kiyayya tsakanin kabilun kasar ko kuma wani mutumi.

KU KARANTA: Sanata Olujimi ta sa Jam’iyyar PDP ta kara yawa a Majalisa

‘Dan takarar PDP na zaben shugaban kasa a 2019, Atiku Abubakar, ta bakin Hadiminsa, Paul Ibe, ya fito ya na sukar yadda ake kokarin kakaba hukuncin kisan kai ga duk wanda aka samu da laifi.

A jawabin tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce majalisar ta wuce gona da iri domin kuwa kundin tsarin mulki ya ba kowane ‘Dan kasa fitowa su fadi duk irin abin da su ka ga dama.

Kungiyoyi masu zaman kansu irin su Free Nigeria Movement da Leadership & Accountability Initiative sun nuna sam ba su goyon bayan wannan kudiri don haka majalisa ta yi watsi da shi.

Kungiyar Lauyoyi watau NBA, ta nuna rashin goyon batanta ga kudirin ta bakin Sakataren yada labaran kungiyar na kasa, Kunle Edun. Wannan shi ne ra’ayin wasu manyan Lauyoyi da-dama.

Tun a cikin majalisar, Sanata Abaribe Enyinnaya mai wakiltar yankin Arewacin jihar Abia ya bayyana cewa Sanatocin PDP ba za su bari a shigo da abin da zai keta hakkin mutane ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel