Ficewar mambobi daga zauren majalisa: Majalisar dattijai da dage zamanta ba shiri

Ficewar mambobi daga zauren majalisa: Majalisar dattijai da dage zamanta ba shiri

A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta dage zamanta babu shiri sakamakon ficewar da tashi daga kujerunsu da kuma ficewa daga zauren majalisar da Sanatocin suka yi, lamarin da ya bar tsirarun mambobi yayin zaman majalisar.

Rashin jin dadin ficewar da mambobin suka yi ne yasa Sanata Abba Moro, mamba mai wakiltar mazabar jihar Benuwe a majalisar, ya mike domin jan hanakalin shugaban majalisar a kan lamarin.

Ya bayyana cewa adadin mambobin da suka rage a zauren majalisar ya gaza kai wa kaso daya cikin uku (1/3) na adadin majalisar, a saboda haka bai kamata a cigaba da tattauna wani batu ba yayin da mafi yawan mambobin majalisar suka fice.

Sai dai, shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan, ya yi watsi da bukatar Sanata Moro tare da bayyana cewa kasancewar babu wasu mambobi a zauren majalisar ba yana nufin cewa basu kai adadin da zasu iya cigaba da gudanar da zamansu ba.

Lawan ya kara da cewa adadin Sanatocin da suka sa hannu a rijistar majalisa ya nuna cewa sun kai adadin da doka ta ambata domin gudanar da zaman majalisa.

DUBA WANNAN: APC: Kotun daukaka kara ta sake kwace kujerar mamba a majalisar wakilai daga Bauchi

Kazalika, ya kara da cewa mai yiwuwa mambobin da basa kan kujerunsu, sun fita shan shayi ne ko kuma sun shiga bandaki.

Da yake magana bayan shugaban majalisar ya kammala jawabi, Sanata Yahaya Abdullahi, ya goyi bayan Sanata Moro tare dabukatar a daga zaman majalisar saboda karancin mambobi a zauren majalisar.

Lawan ya tambayi mambobin da suka rage ra'ayinsu, ta hanyar kuri'ar murya, a kan daga zaman majalisar ko cigaba da shi, kuma suka nuna sun goyi bayan a daga zaman majalisar zuwa ranar Talatar makon gobe.

Majalisar ta daga zaman ne ba tare da shiri ba, saboda akwai sauran kudirai guda biyu da ya dace ta tattauna a kansu, kamar yadda yake a tsarin zamanta na ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel