Faston da matar aure ta yiwa tuhumar fyade: Kotu ta yi watsi da karar, har an ci ta taran N1m

Faston da matar aure ta yiwa tuhumar fyade: Kotu ta yi watsi da karar, har an ci ta taran N1m

Wata babbar kotun birnin tarayya dake unguwar Bwari a ranar Alhamis ta yi watsi da karar da Misis Busola Dakolo ta shigar kan faston cocin Commonwealth of Zion Assembly (COZA), Biodun Fatoyinbo.

Alkalin ya yanke hukuncin cewa babu gaskiya cikin lamarin kuma sai mai zargi, Busola Dakolo, ta biya taran N1,000,000 na batawa kotu lokaci.

Busola Dakolo ta bukaci kotu ta kwato mata hakkinta saboda faston ya yi mata fyade lokacin tana yar shekara 16 a garin Ilori, jihar Kwara.

Tuni faston ya musanta zargin kuma suka garzaya kotu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel