Majalisa: Ahmad Lawan ya rantsar da Sanata Abiodun Olujimi

Majalisa: Ahmad Lawan ya rantsar da Sanata Abiodun Olujimi

A yau Alhamis, 14 ga Watan Nuwamban 2019, Sanata Abiodun Olujimi ta koma kujerarta a majalisar dattawa. Kamar yadda mu ka samu labari Sanatar ta yi rantsuwar shiga ofis dazu.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, shi ne ya rantsar da Biodun Olujimi inda za ta cigaba da wakiltar Mazabar jihar Ekiti ta yamma a majalisa ta tara.

Biodun Olujinmi ta maye gurbin Sanata Adedayo Adeyeye wanda kotu ta karbe kujerarsa. Kotun daukaka kara da ke zama a Garin Kaduna ta ba 'Yar takarar adawar gaskiya a shari’ar zabe.

Idan ba ku manta ba tun a karamin kotun da ke sauraron korafin zaben kasar, Alkalai su ka bayyana cewa ba Dayo Adeyeye ba ne zababben Sanatan Kudancin Ekiti a majalisar dattawa.

KU KARANTA: ‘Dan takaran APC zai tafi kotun koli bayan an ba PDP gaskiya

Da wannan hukunci, matan da ke majalisar dattawan Najeriyar sun kara yawa. Bayan Abiodun Olujimi akwai Sanata Oluremi Tinubu, Uche Ekwunife, Stella Oduah da Aishatu Ahmed.

Sauran matan da ke majalisar sun hada da: Sanata Rose Okoji Oko, Fatimat Raji-Rasaki wanda ita ma ta fito daga jihar Ekiti. Fatimat Raji-Rasaki ta na wakiltar Ekiti ta tsakiya ne a majalisar.

Yanzu jam’iyyar PDP ta karu da Sanata guda a sakamakon rantsar da Olujunmi. Dama can ita ce ta wakilci Mazabar ta a majalisar da ta shude kafin INEC ta ce ta sha kashi a zaben 2019.

Bayan tsige Dayo Adeyeye na APC, jam’iyyar PDP ta koma ta na da Sanatoci fiye da 45. APC mai mulki da rinjaye ta na da sama da 60. YPP mai hamayya kuma ta na da Sanata guda rak.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel