Gasar AFCON 2021: Kungiyar Super-Eagles sun doke Kasar Benin da ci 2-1

Gasar AFCON 2021: Kungiyar Super-Eagles sun doke Kasar Benin da ci 2-1

A wasan da aka buga jiya, Samuel Kalu ya taimakawa Najeriya ta hau saman rukuni na 12 na shirin zuwa Gasar cin kofin Nahiyar Afrika na AFCON wanda za a buga a cikin shekarar 2021.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto cewa Tawagar Najeriya ta doke kasar Benin da ci 2-1. Masu bakunta ne su ka fara dirkawa Najeriya kwalla a raga bayan mintuna uku rak da takewa.

Stephane Sessegnon shi ne wanda ya yi amfani da sakacin ‘yan bayan Najeriya ya koyawa Mai tsaron ragar Super Eagles, Daniel Akpeyi, hankali. Sai dai aka shafe mintuna 40 kafin a rama cin.

Fitaccen ‘Dan wasan Eagles, Samuel Chukwueze, ya kusa kai ga ci bayan da kwallon da ya buga ta yi wa Benin kararrawa, ta bugi karfen raga ta koma. Jim kadan kenan sai Najeriya ta samu rabo.

Yayin da ake shirin tafiya hutun rabin lokaci ne Victor Osimhen ya fara rufawa Najeriya asiri. ‘Dan wasan gaban ya doka bugun daga kai sai mai tsaron gida ne a ragar Saturnin Allagbé.

KU KARANTA: An dakatar da 'dan kwallon Najeriya da ya mari Alkalin wasa

Kalu ne ya sa Najeriya ta tsira da mutuncinta bayan ya shigo cikin wasan daga baya. Matashin ‘dan kwallon da ke bugawa Kungiyar Bordeaux ta Faransa ya jefa kwallonsa ne a minti na 63.

‘Dan wasan gaban mai shekaru 22 da haihuwa ya sheka a guje, ya yanke ‘yan wasan baya uku kafin ya dikara kwallon cikin lilo. Hakan na nufin kasar ta soma wasannin ne da babbar nasara.

A rukunin da Najeriya ta ke ciki, Sierra Leone da Lesotho sun tashi da maki guda ne a jiya bayan Sierra Leone ta kare da yin canjaras Lesotho a wasan da aka buga a babban birnin Freetown.

Namibia, Guinea-Bissau, Central African Republic da kuma kasar Malawi duk sun samu nasara a wasan tsakiyar makon nan. An buga wasan ne a filin Godswill Akpabio na Uyo a Akwa Ibom.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel