Dankari: Yadda ma’aikacin banki ya hada kai da wasu suka yashe wani kwastama bayan sun yi tunanin ya mutu

Dankari: Yadda ma’aikacin banki ya hada kai da wasu suka yashe wani kwastama bayan sun yi tunanin ya mutu

Rahotanni sun kawo cewa wani ma’aikacin banki da wasu mutane uku sun yashe asusun wani mutumin Najeriya da ke zama a kasar Saudiyya.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana cewa masu laifin sun yi zatoncewa mammalakin asusun ajiyan, Sanusi Yakubu, ya mutu sakamakon kwashe tsawon shekaru da ya yi ba tare da amfani da asusun ba.

Daya daga cikin masu laifin, ma’aikacin banki, ya kira abokan ta’adinsa masu suna Ado Shehu, Ali Muhammad da Abba Sanusi, wadanda ke aiki a kotun shari’a, jihar Kano, domin samo takardar kotu da ke nuna cewa mammalakin asusun ya mutu, sannan cewa a matsayinsa na magajinsa, a mallaka masa kudin.

Don haka Sai Yakubu ya shigar da korafi ga ofishin EFCC reshen Kano, wacce tuni ta gurfanar da Shehu da Muhammad a gaban Justis Amina Aliyu ya babbar kotun jihar Kano kan tuhume-tuhume uku da suka hada da sata.

Mai karar, Yakubu, a cikin korafin da ya shigar, ya yi zargin cewa Wani Williams Aondo wanda ya mutu a yanzu, wanda ya kasance ma’aikacin wani banki ya hada kai da Shehu da Mihammad dukkaninsu ma’akatan kotun shari’a, jihar Kano wajen amfani da ikirarin doka cewa shi (Yakubu) ya mutu, bayan Aondo ya lura da rashin amfani da asusunsa na wasu shekaru, alhalin yana raye a kasar Saudiyya.

Yakubu ya kuna yi zargin cewa kotun, wacce ta yi aiki da bayanan da aka gabatar mata ta hannun Shehu da Muhammad, sai ta yi umurnin rufe asusunsa sannan aka mikawa kotun kudin da ke ciki na N1,255,728.00 domin rabawa magadansa.

Wadanda ake tuhumar ba su amsa tuhume-tuhumen da ake masu ba.

Duba ga rokonsu lauyan gwamnati, Zarami Mohammed ya bukaci kotun da ta sanya ranar shari’a sannan cewa a tsare wadanda ake kara a gidan gyara halayya.

Sai dai kuma lauyan wadanda ake tuhuma, Rabiu Sani ya nemi a bayar belinsu, wanda Justis Amina Aliyu ta bayar.

An bayar da belin kan 100,000 kowannensu da mutane bibbiyu da za su tsaya masu.

Ya zama dole daya daga cikin masu tsaya masu y kasance ma’aikacin kotun, sannan dole ya kasance da akalla matsayi na 12.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya na shirin diban ma’aikatan noma 75,000

Ta nemi a tsare su zuwa lokacin da Za su cika sharadin beli.

An dage karar zuwa ranar 14 ya watan Nuwamba domin shari’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel