Innalillahi: Matashin saurayi dan Najeriya ya shake mahaifiyarsa har sai da ta mutu

Innalillahi: Matashin saurayi dan Najeriya ya shake mahaifiyarsa har sai da ta mutu

- Jami'an 'yan sandan jihar Texas sun cafke Eyitoluwa Olayeye, mai shekaru 20 a duniya da laifin kashe mahaifiyarsa

- Ya kasheta ta ne a wani dakin otal da ke Texas kuma ta hanyar shake mata wuya kamar yadda binciken likitoci ya nuna

- Ana zargin saurayin da matsalar kwakwalwa wanda ba a riga an tabbatar ba har yanzu

Ranar Larabar nan da ta gabata ne jami'an 'yan sanda a jihar Texas suka cafke wani saurayi mai shekaru 20, akan laifin kashe mahaifiyarsa a wani otal.

An samu gawar mahaifiyar saurayin mai shekaru 48, mai suna Kehinde Olayeye, da fuskarta kife a kasa tare da danta kwance a bayanta.

A ranar 6 ga watan Oktoba, da misalin karfe 4 na dare aka tura jami'an 'yan sanda wani otal sakamakon hayaniyar da aka jiyo a wani daki na otal din.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, jami'an tsaron sun yi ta buga kofar amma ba bude ba, sai da suka yi amfani da makulli daga hukumar otal din suka bude.

Bayan budewarsun ne suka tarar da matar kwance a kasa da matashin saurayin danta a gefe.

Daga gwaje-gwajen da likitoci suka yi mata sun gano cewa shaketa aka yi wacce tayi sanadiyyar mutuwarta. Ma'aikatan otal din sun bada shaidar sun ji ihun matar tare da kakari da kokarin kwatar kanta.

Kamar yadda kanwar matar ta bayyana, sun samu kira ne daga abokin saurayin, cewa bashi da lafiya kuma an garzaya dashi asibiti daga makaranta.

KU KARANTA: Gwamnati za ta kulle wuraren bauta a jihar Legas saboda suna damun mutane da hayaniya

Bayan wani lokaci sai aka kirasu daga asibitin ake tambayar su ko saurayin yana da wata matsala ta tabin kwakwalwa?

Tuni mahaifiyarsa da kanwarta suka kamo hanyar zuwa Texas. Suna kan hanya ne abokin yake sanar dasu an sallamesu daga asibitin.

Bayan isowarsu gidan abokin, sun tattauna inda suka tashi don samun otal din da zasu kwana.

Kanwar mahaifiyar ta sa ta ce, sun raba dare suna hira, inda daga baya ta tafi dakinta ita kadai. Ta bar saurayin da mahaifiyarsa wanda bayan hakan ne mummunan labarin ya iske ta da goshin asuba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel