Yadda dalibin jami'ar Legas ya harbi wani mutum a mazakuta

Yadda dalibin jami'ar Legas ya harbi wani mutum a mazakuta

Wani dalibin jami'ar jihar Legas, a ranar Laraba ya gurfana a gaban kotun laifuka na musamman a Ikeja. An gurfanar da shi ne akan zarginsa da ake da fashi da makami tare da harbin wani mutum mai suna Oke Oscar, a mazakutarsa.

An gurfanar da Saheed ne tare da wasu mutane biyar da ake zargin 'yan kungiyar 'Aiye Confraternity' ne. Wadanda ake zargin su ne: Victor Otobo, Suleiman Musa, Ibrahim Kolade, Ayinla Muiz da Lateef Alowonle. Ana zarginsu da alifuka 11 ne da suka hada da, hadin kai wajen fashi da makami, yunkurin kisan kai tare da nakasa wani.

Sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su.

An gano cewa, wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Satumba 2018 wajen karfe 8:40 na dare, a yankin bututun man fetur na jami'ar jihar Legas. Sun aikata wani laifin kuma a ranar 2 da 4 ga watan Oktoba, 2018 wajen karfe 9 na dare a titin Ahiawu Apeke na yankin Okokomaiko.

DUBA WANNAN: Wani mutum ya sari kaninsa da adda kan zargin yana kwartanci da matansa (Hoto)

Dan sanda mai kara, Olakunle Ligali, ya ce laifukan sun ci karo da sashi na 299, 297, 230 da kuma 245 na dokokin laifukan jihar Legas na 2015.

Laifukan su ne, "Shittu Saheed, Suleiman Musa, Ibrahim Kolade, Ayinla Muiz da Lateef Alowonle, a otal din Dubai na yankin bututun man fetur na Okokomaiko, suna cikin kungiyar asiri mai suna Aiye Confraternity ko Black Axe,"

"Su biyar din a ranar 2 ga watan Oktoba a wajen karfe 9 na dare a titin Ahiawu Apeke na yankin Okokomaiko, sun illata Oke Oscar sakamakon harbinsa da suka yi a mazakuta da bindigar gargajiya".

Alkalin kotun, Jastis Josephine Taiwo, ya dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Disamba 2019 don cigaba da zaman kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel