Huce haushin shan kashin 2019 ya sa ake so a tuhumi Tinubu - Matasan APC

Huce haushin shan kashin 2019 ya sa ake so a tuhumi Tinubu - Matasan APC

Wata kungiya ta Matasan jam’iyyar APC a Najeriya, ta yi kira ga jam’iyyar hamayya ta PDP da ta yi wa ‘ya ‘yanta kashedi su daina huro wuta cewa a binciki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A wani jawabi da kungiyar APC National Awareness for Youth Vanguard ta fitar a Ranar Laraba, 13 ga Watan Nuwamba, 2019, ta soki kiran da ake yi wa hukumar EFCC ta bi ta kan Jagoranta.

Shugaban wannan kungiya ta Matasan APC, Alhaji Muktar Abubakar, ya bayyana cewa ana neman EFCC ta binciki Bola Ahmed ne saboda ya bada gudumuwa wajen lallasa PDP a 2019.

Wata kungiya mai zaman kan-ta, ta bukaci EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta binciki abin da ya kai motar kudi cikin gidan Bola Tinubu a lokacin zaben bana.

KU KARANTA: Uwar Jam’iyya ta fatattaki Shugaban APC na jihar Edo

Abubakar ya fitar da jawabi ya na cewa: “Abin da mu ka gani shi ne wasu masu neman-suna sun fito su na jefa zargi a kan daya daga cikin ‘yan siyasan da ake ganin darajar su Najeriya a yau.”

Jawabin ya kara da: “Neman EFCC ta binciki Jagoran jam’iyyar APC saboda ya ajiye motar kudi a gidansa, tun kafin ayi nisa ba zai kai ko ina ba, haka kuma wannan ikirari bai da gindin zama."

Dalilin cewa haka kuwa shi ne babu wanda ya taba zargin hanyar arzikin Jagoran na APC saboda ya mika kansa gaban hukuma har sau biyu a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan Legas.”

Bayan gabatar da kadarorinsa a lokacin da ya ke mulkin jihar Legas, kungiyar ta bakin Alhaji Muktar Abubakar tace ‘Yan Najeriya sun san labarin duk kamfanin da ‘dan siyasar ya mallaka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel