Jami’an NDLEA sun yi ram da wani gagararren dillalin miyagun kwayoyi a Imo

Jami’an NDLEA sun yi ram da wani gagararren dillalin miyagun kwayoyi a Imo

Hukumar yaki da sha da fatauci da miyagun kwayoyi reshen jahar Imo ta samu nasarar kama wani kasurgumin gagararren dillalin miyagun kwayoyi mai suna Uzochi Agbakwuru, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Kaakakin hukumar NDLEA na jahar Imo, Uche Sampson ne ya sanar da haka a ranar Laraba, yayin da yake ganawa da manema labarun, inda yace a ranar 18 ga watan Oktoba suka kama Uzochi, kuma yana hannunsu.

KU KARANTA: Iyaye sun daina aurar da ‘ya’yansu mata a Kano saboda dokar kayyade sakadin aure

A jawabinsa, Mista Uche ya bayyana Uzochi a matsayin gagararren mai safarar miyagun kwayoyi a jahar, don hakaya nuna bacin ransa da wani takarda da wani mutumi Frank Agbakwuruibe ya rubuta yana neman gwamnan Imo, Emeka Ihedioha ya umarci NDLEA ta saki Uzochi.

“Mun kwashe tsawon watanni 18 muna farautar Uzochi, kuma duk kokarin da muka yi a baya na kama shi ya ci tura sakamakon yana da yan leken asiri da bashi bayanan sirri. Mun kama shi da giram 150 na tabar wiwi, wanda hakan ya saba ma dokar NDLEA.” Inji shi.

Kaakakin yace a cikin gidansa suka kama Uzochi, kuma ya yi kokarin tserewa ta hanyar gayyato abokansa da jama’an unguwarsu domin su kawo masa dauki, wanda hakan yasa kazamin rikici ya kaure tsakaninsu da jami’an NDLEA.

Daga karshe kaakakin yace tuni hukumar NDLEA ta gurfanar da Uzochi gaban babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Owerri, babban birnin jahar Imo.

A wani labari kuma, Mmiyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun halaka wani mutumi mai suna Hamza Abubakar Mahuta bayan sun karbi kudin fansa daga hannun yan uwansa, kudin da ya kai naira dubu 500.

Hamza Mahuta jami’i ne hukumar kula da dokokin hanya ta jahar Kaduna, wanda yan bindigan suka yi awon gaba da shi a ranar 16 ga watan Oktoba a kan hanyar Birnin Gwari yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida wajen iyalansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel