Adelabu ya dumfari kotun koli a kan shari’ar zaben Gwamnan Oyo

Adelabu ya dumfari kotun koli a kan shari’ar zaben Gwamnan Oyo

‘Dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaben jihar Oyo, Adebayo Adelabu, ya ce zai shigar da kara a gaban kotun koli domin karbo nasararsa a zaben 9 ga Watan Maris, 2019, da aka yi.

A Ranar 13 ga Watan Numwaba, aka rahoto ‘dan takarar ya na cewa zai kalubalanci hukuncin kotun daukaka kara wanda ya tabbatar da gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya ci zabe.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana, Mista Adebayo Adelabu, ya fitar da jawabi yana cewa wasu mutane ne su ka shiga su ka fita domin har aka karbe masa nasarar da ya samu a zaben da aka yi.

Adelabu ya ke cewa fashin da aka yi masa a zaben gwamnan ya sa ya ke neman kotu ta karbo masa hakkinsa. Sai dai kotun sauraran karar zabe da na daukaka kara sun yi watsi da korafinsa.

Ya ce: “Ta tabbata mun tsara yakin neman zabe nagari inda mutane su ka gamsu da tafiyarmu, su ka fito su ka bamu kuri’arsu. Amma wasu mugaye su ka tsara yadda za a karbe mana nasara.”

KU KARANTA: Gwamna zai fara biya sabon tsarin albashin Ma'aikata kwanan nan

Jawabin ya kara da cewa: “Karamar kotun sauraron korafin zaben sun damu kansu da wasu kuci-kucin abubuwa a maimakon tarin abin da mu ka gabatar don haka su ka yi fatali da kararmu.”

“A dalilin haka mu ka tafi kotu domin mu fallasa barnarsu. Yanzu tun da kotun daukaka kara ma ta tabbatar da rashin daidai a matsayin daidai, ina ba mutanenmu hakuri, za mu tafi kotun koli.”

‘Dan takarar ya yi kira ga jama’a da su ka cigaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali tare da ba su tabbacin cewa za su samu nasara a hannun Alkalan babban kotun kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel