Uwargida ta shigar da karar Maigida saboda yana yi ma kananan yara fyade a Kaduna

Uwargida ta shigar da karar Maigida saboda yana yi ma kananan yara fyade a Kaduna

Wata mata mai suna Fatima Ishaq ta gurfanar da mijinta, Hassan Haruna gaban wata kotun addinin Musulunci dake garin Kaduna, inda take zarginsa da laifin yi ma wata karamar yarinya fyade tare da tilasta mata kwanciya da shi.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa matar wanda take zaune da mijinta a wata unguwa dake cikin garin Kaduna ta bayyana ma kotu ta bakin lauyanta, M.S Abdullahi cewa ba zata iya cigaba da zama da Hassan a matsayin mijinta ba.

KU KARANTA: Inda ranka ka sha kallo: Mutumin da ya yi aure sau 60 a shekaru 25 ya shiga hannun Yansanda

Lauyan ya bayyana ma kotu cewa wanda yake wakilta ba zata baiwa kotu tabbacin cigaba da ganin girman mijin nata ko girmama shi ba, don haka ta ke neman kotu ta sawwake mata zama da Hassan.

Lauyan ya kara shaida ma kotu cewa a shirya Fatima take ta biya Hassan sadakin aurenta da ya biya N5000 a shekarar 2006, sa’annan ta roki kotu ta bata rikon yaransu guda 4, tare da bukatar mijin ya dinga biyanta N20,000 a duk wata domin kulawa da yaran.

Sai dai a yayin da aka gurfanar da Hassan a gaban kotu, ya musanta zargin da ake masa na yi ma karamar yarinya fyade, inda yace: “In dai saboda zargin fyade da ake min ne kike so ki rabu dani, zan iya rantsewa da Al-Qur’ani ban aikata laifin nan ba, amma zan amince da bukatar ki ta neman saki.”

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkalin kotun, Dahiru Lawal ya kashe auren ma’auratan, sa’annan ya umarci Fatima ta biya Hassan N15,000 a matsayin sadakin da ya biya lokacin da zai aureta, saboda darajar N5000 daya biya a shekarar 2006 ya karu a yanzu.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan kasar Bangladesh ta kama wani mutumi dan shekara 45 mai suna Abu Baker sakamakon kararsa da matarsa ta shigar gaban Yansanda inda take zarginsa da aure sau 60 a cikin shekaru 25.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel