Kotu: Za a rataye wadanda su ka sace Sarkin kasar Iba a 2016 har lahira

Kotu: Za a rataye wadanda su ka sace Sarkin kasar Iba a 2016 har lahira

Alkalin babban kotun tarayya da ke Legas, Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo, ya yankewa wasu mutane hukuncin kisan kai. Alkalin ya same su ne da laifin sace Mai marataba Goriola Oseni.

Oba Goriola Oseni shi ne Sarkin Iba wanda aka sace shi a cikin Watan Yulin shekarar 2016. Mai martaban ya yi makonni a hannun masu garkuwa da mutanen, har sai da aka biya kudin fansa.

Rahotannin sun ce wadanda aka yankewa hukuncin su ne Duba Furejo, Ododomo Isaiah, Reuben Anthony, da Yerin Fresh. An gurfanar da su a gaban kuliya ne tun shekaru uku da su ka wuce.

Gwamnati ta na zarginsu da laifuffuka takwas wadanda su ka hada da kisan-kai, yunkurin kisa, fashi da makami, garkuwa da mutum da sauransu. A karshe kotu ya same su da laifi dumu-dumu.

Ana zargin wadanda ake tuhumar da hallaka wani Mai gadi a fadar Sarkin mai suna Sunday Okanlawon. Sannan kuma sun kashe ‘Dan acaba, Joseph Okeke, a lokacin da su ka yi ta’adin.

KU KARANTA: An gurfanar da wani Surukin Atiku Abubakar a gaban Alkali

Haka zalika Lauyoyi sun zargi Furejo, Ododomo Isaiah da sauran Abokan aikin na sa da yi wa Mai dakin Sarkin kasar Iba fashi inda su ka sace mata wayar salula sannan kuma su ka harbe ta.

Alkali ya saurari shaidu bakwai da gwamnati ta kawo domin su tabbatar da zargin. A karshe Alkali mai shari’a Toyin Taiwo ya tabbatar da cewa kotu ta sami wadanda ake tuhuma da laifi.

A Ranar 13 ga Watan Nuwamba, 2019, aka yanke hukunci cewa a rataye wanda ake zargin a sakamakon kashe Sunday Okanlawon da kuma Joseph Okeke da su ka yi a cikin shekarar 2016.

Sannan kuma Alkalin ya kara masu da hukuncin daurin rai da rai saboda harbin Sede Goriola, da daurin shekaru 10 na shirya yin kisa, game da wasu karin shekaru 10 na garkuwa da mutane.

Kotu ta kuma yankewa wadanda ake karar hukuncin daurin rai da rai da shekaru 21 a gidan yari a matsayin ukuba na laifin fashi da makami. Da farko dai duk sun musanya zargin da ake yi masu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel