Bayelsa: ‘Yan daba sun kashe wani ‘Dan jarida, an raunata da-dama

Bayelsa: ‘Yan daba sun kashe wani ‘Dan jarida, an raunata da-dama

A Ranar Larabar nan ne Jaridar This Day ta rahoto cewa an kashe wani ‘dan jaridar a wajen taron da jam’iyyar PDP ta shirya na yakin neman zaben gwamna a Garin Nembe a cikin jihar Bayelsa.

Rahotannin sun ce an kashe Simon Onu, wanda ya ke aiki a gidan rediyon Bayelsa. Haka zalika an yi wa wasu mutane da-dama rauni, yanzu haka wasunsu su na kwance a asibitocin da ke Yenogoa.

Onu ya na kusa ne da wani ‘dan bindiga wanda ya dana masa dalma har lahira. Hakan ya faru a lokacin da ya ke kokarin tserewa cikin motarsa domin tsira da ransa a lokacin da aka fara harbe-harbe.

Wannan mummunan abu ya faru ne a Garin Ogbolomabiri inda rigima ta kaure wajen kamfe yayin da ake jiran isowar gwamna Seriake Dickson da kuma ‘dan takarar PDP a zaben, Sanata Douye Diri.

KU KARANTA: An kona motar Jami'an 'Yan Sanda a Jihar Kaduna

Wadanda rikicin ya faru a idanunsu, sun ce Mista Olu ya mutu nan-take ne bayan an harbe sa. Marigayin ya zo wurin ne da motar aiki da nufin daukar rahoton yadda yakin neman zaben ke gudana.

Wadannan miyagun mutane sun tada zaune tsaye ne a filin wasa na King Koko Square bayan an shirya tsaf domin karbar manyan ‘yan PDP. Garin Ogbolomabiri dai na neman ya zama abin da ya zama.

Kwanakin baya idan ba ku manta ba, kun ji cewa wasu ‘yan daba sun kai wa motar gidan gwamnati hari a daidai mahadar Bassambiri da wannan Gari na Ogbolomabiri da ke gabashin Bayelsa.

Jami’an tsaro ba su ce komai ba tukuna don haka kawo yanzu ba mu samu adadin mutanen da aka hallaka ba. Ana rade-radin cewa an kashe mutane shida, yayin da wasu da-dama su ke jinya a asibiti.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar ta Bayelsa, Asinim Bustwat, bai ce komai ba a lokacin da ‘yan jarida su ka tuntubesa. Amma mun ji cewa an aika Dakarun Sojoji domin a shawo kan rikicin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel