Oshiomhole ya bude wuta, NWC ta dakatar da Shugaban APC a Jihar Edo

Oshiomhole ya bude wuta, NWC ta dakatar da Shugaban APC a Jihar Edo

A wajen wani zama da majalisar NWC ta shugabannin jam’iyyar APC mai mulki ta yi, ta yi na’am da matakin da jam’iyyar ta dauka a jihar Edo na dakatar da shugabanta watau Anslem Ojezua.

Adams Oshiomhole ne ya jagoranci wannan zama na NWC da majalisarsa inda su ka sa hannu a kan fatattakar da shugabannin APC su ka yi wa Anslem Ojezua daga cikin tafiyar jam’iyyar.

Kamar yadda Sakataren yada labarai na APC na kasa, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana bayan taron, ya ce uwar jam’iyya ta duba lamarin da ya auku a Edo inda aka dakatar da shugaban jam’iyya.

Malam Lanre Issa-Onilu ya tabbatar da cewa uwar jam’iyyar ta rattaba hanu kan dakatarwar da aka yi wa Anslem Ojezua ganin cewa matakan da jam’iyyar ta reshen Edo ta bi, sun cika ka’ida.

Yanzu APC ta amince da dakatarwar da aka yi wa shugabanta na bangaren jihar Edo inda ta ke jiran rahoton da kwamitin bincike da sulhun da aka nada zai yi domin gano shawo kan matsalar.

KU KARANTA: An haramtawa APC tsayawa takara a zaben Gwamnan Bayelsa

Jagororin jam’iyyar APC 11 cikin 16 da ake da su a majalisar SWC na jihar Edo ne su ka sallami Mista Anslem Ojezua daga jam’iyyar. Ba a fadi iyakar wa’adin wannan dakatarwar da aka yi ba.

Idan ba ku manta ba kafin a kai ga wannan zama, wasu daga cikin majalisar zartarwa na jam’iyyar APC a jihar ta Edo, sun dauki matakin dakatar da Adams Oshiomhole daga reshensu.

NWC ta jam’iyyar APC ta duba abin da ya faru a jihar Edo cikin takaici kuma ta damu da yadda abubuwa su ka kaure. Wannan ya faru ne duk da kokarin da shugaban gwamnoni ya yi na sulhu”

Issa Onilu ya kara da cewa bayan yunkurin Kayode Fayemi, shugaban gwamnonin APC, Abubakar Bagudu, ya nemi ya sasanta rikicin amma bai yiwu ba, har abin ya kai zuwa wannan hali.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel