Gwamnati za ta kashe naira biliyan 900 don gudanar da manyan ayyuka a watan Disamba

Gwamnati za ta kashe naira biliyan 900 don gudanar da manyan ayyuka a watan Disamba

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatarta za ta fitar da makudan kudi naira biliyan 900 domin gudanar da manyan ayyuka.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Ministar ta bayyana haka ne a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba yayin da take ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar zartarwar Najeriya.

KU KARANTA: Garkame iyakokin Najeriya: Majalisa ta umarci Hamid Ali ya gurfana a gabanta

Taron na majalisar zartarwar ya gudana ne a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, a fadar gwamnatin Najeriya dake Aso Rock Villa, a babban birnin tarayya Abuja, wanda ya samu halartar kafatanin ministocin Najeriya.

Shamsuna ta ce zuwa yanzu ma’aikatarta ta saki kudi naira biliyan 650 domin gudanar da manyan ayyuka tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarceta game da hakan a watan Oktoba, jim kadan bayan ya mika kasafin kudi ga majalisa.

Ministar tana wannan bayani ne biyo bayan maganan da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ya yi game da rashin samun isassun kudade wajen gudanar da dimbin manyan ayyukan da gwamnati ta sanya a gaba.

Sai dai Ministar kudi ta amince da batun da ministan ayyuka ya yi, amma tace duk da haka gwamnati na baiwa ma’aikatar ayyuka da ma’aikatar sufuri kulawa ta musamman wajen basu kudi domin gudanar da manyan ayyuka.

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban hukumar yaki da fasa kauri na Najeriya, Hamid Ali da ya gurfana a gabanta don tsatstsage mata bayani game da matakin haramta kai man fetir zuwa ga yankunan iyakokin Najeriya.

Majalisa ta bayar da wannan umarni ne ga kwamitinta dake kula da hukumar kwastam a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, biyo bayan kudurin da Sanata Odebiyi Akinremi dan jam’iyyar APC daga jahar Ogun ya gabatar gaban majalisar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel