Gwamnati za ta kulle wuraren bauta a jihar Legas saboda suna damun mutane da hayaniya

Gwamnati za ta kulle wuraren bauta a jihar Legas saboda suna damun mutane da hayaniya

- Domin shawo kan matsalar hayaniya a jihar Legas, gwamnatin jihar ta ce ba zata yi kasa a guiwa ba wajen rufe duk wajen da ke haddasa hayaniya

- Wuraren sun hada da masallatai, majami'o'i, gidajen rawa da sauran wuraren shakatawa

- Ma'aikatar muhalli ta jihar ta shawarci cibiyoyin bauta da shakatawa da su samu kayan sauti masu daidaita amo

Domin shawo kan matsalar hayaniya, gwamnatin jihar Legas ta ce, ba zata yi kasa a guiwa ba wajen rufe duk masallatai, majami'u, gidajen rawa da sauransu, da ke bada gudummawa wajen damun muhalli.

Kwamishinan muhalli da ruwa, Tunji Bello, a jawabinsa jiya, ya bayyana cewa, cibiyar kare muhalli ta jihar Legas (LASEPA) ta dau nauyin tabbatar da bin dokar.

Ya ce, daukar mataki ya zama dole sakamakon koke da kararrakin da mutane tare da kungiyoyin da ke fadin jihar ke kawowa akan yawan hayaniya da guraren shakatawa da gidajen addinai ke fitarwa.

Bello, ya kara da cewa, jami'an LASEPA zasu cigaba da zagaya cibiyoyin addini da sauransu, don jan kunnen duk wanda suka kama da laifin inda daga baya zasu rufe wajen tare da hukuncin da ya dace.

KU KARANTA: Tashin hankali: Birai sun afka wani kauye suna duka da kashe mutane haka siddan

Kwamishinan ya kara da jajanta yadda ofishinsa ya gano cewa, guraren shakatawa da yawa bayan an rufesu, akan basu damar kara budewa amma sai su cigaba da hayaniyar da ta sa aka rufe su din.

Yayin bayaninsa, ya ce duk wajen da gwamnati ta rufe saboda hayaniya, ba za a kara budeshi ba, ba tare da wasikar yardar mutane ko kungiyar yankin ba.

Ya shawarci cibiyoyin addinai da guraren shakatawa, da su samu kayan sauti marasa tashi wadanda zasu rage hayaniyarsu.

Bello ya ce, gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ba zata amince da duk wata harka da zata hana walwalar mutane ba kowacce iri ce kuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel