Tashin hankali: Saurayi ya kashe dan uwanshi na jini saboda ya zagi budurwarshi

Tashin hankali: Saurayi ya kashe dan uwanshi na jini saboda ya zagi budurwarshi

- Wannan mummunan lamarin ya faru ne a garin nan da ya zama babbar cibiyar kasuwanci a yankin kudancin Najeriya Onitsha cikin jihar Anambra

- Budurwa ta kai wa saurayi karar kaninsa akan zaginta da yayi kuma baya ganin mutuncinta

- Tuni yayan ya fusata tare da ikirarin sai ya kashe kanin, hakan kuwa ta faru don ya halakasa har lahira

Jaridar Information Nigeria ta gano cewa, wannan al'amarin ya faru ne a babban birnin nan da ya zama cibiya ta kasuwanci wato garin Onitsha dake jihar Anambra.

Kamar yadda wata hirar kafar sada zumunta ta WhatsApp ta nuna, budurwar mai suna Uzor ta kaiwa saurayin nata karar kaninsa mai suna Emeka akan baya ganin mutuncinta kuma yana zaginta.

Fushin hakan ne kuwa yasa Uzor ya kudiri niyyar ladaftar da kaninsa, a sakamakon hakanne kuwa Emeka ya rasa ransa.

Karar da budurwar ta kai ita ce sanadiyyar haddasa fada tsakanin 'yan uwan.

A yayin da suke fadan ne Uzor ya dauki wuka ya bi kanin nasa da ita har yayi nasarar soka masa.

KU KARANTA: Bidiyo: Wani Kirista ya kone Bible ya ce babu wani abu a cikin littafin sai karya

Ga dai abinda jaridar ta rubuta a kasa:

"Budurwar Uzor ta kai masa korafin kaninsa mai suna Nnaemeka cewa ya zageta kuma ba ya ganin mutuncinta, duk kuwa da cewa da Uzor da Nnaemeka basa zama inuwa daya."

"Wannan korafi da budurwar ta kai wa Uzor yasa ya fusata, hakan yasa fada ya sarke tsakanin 'yan uwan, Uzor ya dauko wuka ya bi Emeka da ikirarin sai ya kashe shi, hakan kuwa lamarin ya faru, saboda ya halakashi har lahira."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel