Babbar magana: Ban san uban me mahaifina yake yi ba har su Dangote suka yi kudi suka barshi - Tonto Dikeh

Babbar magana: Ban san uban me mahaifina yake yi ba har su Dangote suka yi kudi suka barshi - Tonto Dikeh

- Fitacciyar jarumar nan ta masana'antar Nollywood, Tonto Dikeh tace tana mamakin Inda mahaifinta yake lokacin da Otedola da Dangote ke tara dukiya

- Jarumar ta wallafa hakan ne a shafinta na Instagram inda ta yi godiya tare da addu'a ga hamshakin mai kudin

- Ta bayyana cewa, mahaifinta ya roki kyan fuska ne lokacin da irinsu Dangote da Otedola ke rokar arziki

Fitacciyar jarumar masana'antar Nollywood, Tonto Dikeh ta ce, tana mamakin abinda mahaifinta yake yi lokacin da Femi Otedola, Aliko Dangote da sauran hamshakan masu kudi suke tara dukiya.

Jarumar ta bayyana haka ne yayi da take magana akan tallafin naira biliyan biyar da Femi Otedola ya bada don taimako ga yankin arewa maso gabas wadanda rikicin Boko Haram ya addaba.

Kamar yanda ta wallafa a shafinta na Instagram jarumar ta ce, "Naira biliyan biyar! A'a banji haushi ba, kawai dai ina nan ina tunanin me mahaifina yake yi lokacin da su Dangote ke tara dukiya? Ina jin shi iya kyakkyawar fuska kadai ya roki ubangiji ya manta bai roki dukiya ba, saboda na san shi kyakyawa ne."

KU KARANTA: Tirkashi: Budurwa ta bayyana yadda babban abokinta dan luwadi ya kwace mata saurayin da take shirin aura

"Allah ubangiji yayi wa Otedola albarka da kuma duk mutanen da ya taimakawa, ina fatan zaka tallafawa sauran wuraren da suke neman taimako."

A wani bikin gala na wata gidauniyar tallafin da Florence Otedola ya shirya, tare da hadin guiwar kungiyar Save the Children dake kasar Birtaniya, na yaran da suka yi gudun hijira daga arewa maso gabas a Najeriya, Otedola ya bada tallafin naira biliyan biyar inda Aliko Dangote ya bada tallafin naira miliyan 100.

Taron ya samu halartar Yemi Osinbajo mataimakin shugaban kasar Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel