'Yan bindiga sun kone motar 'yan sanda a Kaduna

'Yan bindiga sun kone motar 'yan sanda a Kaduna

Wasu mutane da ake zargin cewa 'yan bindiga ne sun kai hari tare da saka wa wata motar 'yan sanda wuta a tsakanin kauyukan Kwanar Labi zuwa Udawa masu makwabtaka da dajin Kwaru a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa majiyarta ta sanar da ita cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na dare bayan an yi musayar wuta a tsakanin 'yan bindigar da jami'an 'yan sanda a yayin da suke kan hanyarsu ta koma wa Kaduna daga Birnin Gwari.

'Yan bindiga na yawan kai hari a kan ababen hawa da ke bin babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, inda suke cin karensu babu babbaka ta hanyar kashe matafiya ko kuma su yi garkuwa da su.

Wata majiya ta sanar da rahoton jaridar Daily Trust cewa dan sanda daya ya samu rauni yayin da ragowar suka gudu zuwa cikin jeji.

DUBA WANNAN: Bayelsa: Kotu ta haramta wa dan takarar APC shiga zaben gwamna na ranar 16 ga wata

"Jami'an 'yan sandan na cikin wata babbar mota ne a daidai lokacin da 'yan bindigar suka kai musu hari a wani wuri da ake kira Kwaru da ke daf da kauyen Udawa bayan an bar Kwanar Labi."

"Daya daga cikin 'yan sandan ya samu rauni, yayin da ragowar suka ruga zuwa cikin daji. 'Yan bindigar na da yawa. Babu asarar rai, amma sun kone motar 'yan sandan," a cewarsa.

Kazalika, wani mazaunin garin Birnin Gwari da bai yarda a ambaci sunasa ba, ya sanar da Daily Trust ta wayar tarho cewa 'yan bindigar sun kone motar jami'an 'yan sandan kurmus.

"Na ga motar na ci da wuta saboda nima na yi tafiya a ranar, amma bamu tsaya ba saboda wurin da abin ya faru, wuri ne mai hatsarin gaske," a cewarsa.

Da aka tuntube shi, mukaddashin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Sulaiman Abubakar, ya ce ba zai yi magana akn faruwar lamarin ba har sai ya samu cikakken bayani a kan abinda ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel