Da duminsa: Kotun Koli ta zabi ranar bayyana dalilin da yasa tayi watsi da karar Atiku

Da duminsa: Kotun Koli ta zabi ranar bayyana dalilin da yasa tayi watsi da karar Atiku

Kotun kolin Najeriya, a ranar Laraba, ta zabi ranar Juma'a, 15 ga Nuwamba domin yiwa duniya bayanin dalilin da yasa tayi watsi da karar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, kan nasarar zaben shugaba Muhammadu Buhari.

Kwamitin Alkalai bakwai karkashin jagorancin shugaban Alkalan Najeriya, CJN Tanko Muhammad, sun bayyana cewa ba da dadewa ba zasu bada dalilin watsi da karar.

Bayan kotun zaben shugaban kasa ta yi fatali da karar jam'iyyar PDP da Atiku a A ranar 11 ga Satumba, tsohon shugaban kasan tare da jam'iyyarsa suka garzaya kotun koli ranar 23 ga Satumba, 2019.

A ranar 30 ga Oktoba, Kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar suka yi wacce ke kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da ya gudana.

KU KARANTA: Mumunan hadari ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 da daren nan

Kungiyar alkalan bakwai na babbar kotun ta ce, sun sakankance cewa babu wani amfani game da daukaka karar. A don haka ne suka yi fatali da karar.

Tsokaci kan lamarin, Atiku ya bayyana bacin ransa da takaici kan yadda bangaren shari'a, yan jarida, da hukumar zabe ta INEC ba su da karfi a Najeriya.

Atiku ya ce wannan shari'a ya nuna cewa dukkan abinda PDP ta gina a shekaru 16 da tayi mulki na kawo cigaban demokradiyya, wannan gwamnatin ta rusa su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel