Yanzu-yanzu: Mumunan hadari ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 da daren nan

Yanzu-yanzu: Mumunan hadari ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 da daren nan

Hukumar kiyaye hadura wato FRSC shiyar jihar Ogun ta sanar da mumunan hadarin da ya auku da babban titin Legas zuwa Ibadan da yammacin nan inda aka rashin rayuka 13.

Hukumar ta bayyana cewa hadarin ya faru ne garin Ogere, jihar Ogun kuma mutane 37 ke cikin motocin da ya shafa.

Hadarin ya auku ne tsakanin kananan motoci biyu da babbar mota tirela daya.

Hakazalika mutane goma sun samu raunuka iri-iri kuma an garzaya da su asibitin Victory dake Ogere, jihar Ogun.

DUBA NAN: Ba ni da gida a kasar waje saboda asarar kudi ne - Dangote

Jawabin hukumar yace: "Mumunan hadarin ya shafi mutane 37 wanda ya kunshi maza 20, mata 20 da kananan yara mata 2.

"Mutane goma sun jikkata wanda ya kunshi maza 4, mata 6, kuma an yi rashin mutane 13 wanda ya kunshi maza 4, mata 7 da kanan yara mata biyu."

"Motocin da sukayi hadari sune mota bas kirar Mazda mai kalan ruwa kwai da lamba KTU93XW, Toyota Bas mai lamba KEY847XA da babbar motar mai."

"An bukaci iyalan wadanda suka jikkata su tuntubi ofishin FRSC dake Ogere, Ogun ko asibitin Victory dake Ogere, inda aka kai wadanda suka jikkata domin jinya."

"An kai gawawwakin wadanda suka mutu dakin ajiye gawawwakin Ipara."

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel