Garkame iyakokin Najeriya: Majalisa ta umarci Hamid Ali ya gurfana a gabanta

Garkame iyakokin Najeriya: Majalisa ta umarci Hamid Ali ya gurfana a gabanta

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban hukumar yaki da fasa kauri na Najeriya, Hamid Ali da ya gurfana a gabanta don tsatstsage mata bayani game da matakin haramta kai man fetir zuwa ga yankunan iyakokin Najeriya.

Majalisa ta bayar da wannan umarni ne ga kwamitinta dake kula da hukumar kwastam a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, biyo bayan kudurin da Sanata Odebiyi Akinremi dan jam’iyyar APC daga jahar Ogun ya gabatar gaban majalisar.

KU KARANTA: Kasar Amurka ta bayyana aniyarta na tabbatar da an yi zaben gaskiya a Bayelsa

Sanata Akinremi ya bayyana ma majalisar cewa akwai bukatar hukumar kwastam ta sake gudanar da nazari a kan wannan mataki da ta dauka, saboda rashin kai man fetir zuwa yankunan iyakokin Najeriya ya janyo wahalar mai da kuam tashin farashin man.

Da wannan ne majalisar ta amince da kudurin Sanata Akinremi, inda ta nemi kwamitin majalisar dattawa dake kula da hukumar kwastam ta gayyaci shugaban kwastam Hamid Ali domin su sake duba wannan umarnin kwastam a tare don a samar da mafita.

Haka zalika majalisar ta yi kira ga shugaban kwastam da lokaci ya yi da hukumar za ta fara amfani da kayan aiki na zamani na kimiyya da fasaha wajen bin kadin kayayyaki tare da bincikensu, musamman ma manyan motoci dake daukan mai zuwa iyakokin Najeriya.

Daga karshe majalisar ba jaddada akwai bukatar a samu cikakken bayani game da adadin gidajen mai dake aiki a iyakokin Najeriya domin ta haka ma za’a samu saukin wannan matsala.

A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa majalisar ka iya kammala aikin tabbatar da kasafin kudin shekarar 2020 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba.

Shugaban majalisar ya bukaci kwamitin kasafin kudi na majalisar ta gaggauta mika ma majalisa rahotonta zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba domin cimma wannna manufa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel