Ba ni da gida a kasar waje saboda asarar kudi ne - Dangote

Ba ni da gida a kasar waje saboda asarar kudi ne - Dangote

Shahrarren dan kasuwa kuma mafi arziki a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana dalilin da yasa bai da gida a kasar waje duk da cewa wasu ma'aikatansa sun mallaki manyan gidaje a kasashen waje.

A cewar Celebrity Buzz, Dangote yayi wannan jawabi ne a taron tattaunawar Mo Ibrahim inda yace yakan guji abubuwan jin dadi saboda su kan bata masa lokaci.

Dangote yace: "Ba ni wani gidan zuwa hutu a ko ina. Ba ni da gida a wani waje amma na san wasu ma'aikatana na da gidaje a Landan."

"Idan ka lura, mutane da dama, har da masu kananan shekaru, ya kamata muyi hankali saboda babban matsalarmu yan Afrika shine kashe kudin da muke samu."

Mutum na fara kasuwancin yana samun riba, maimakon kara sanya kudin cikin kasuwancin, sai ya fara kashewa tunanin cewa abubuwa za su cigaba da kyau."

"Akwai rashin tabbas cikin kasuwanci saboda haka ya kamata ku mayar da hankali."

DUBA NAN: Kuma dai! An kashe yan sanda 3 a jihar Kaduna

Yayinda aka tambayeshi kan shin wani sashen zai baiwa kananan yan kasuwa shawara sun sanya hannun jari,Dangote yace: "Bangarorin da ya kamata mayar da hankali kai sune ilimin ICT da aikin noma."

Aliko Dangote ya bayyana cewa yawancin mutane basu iya taimaka ma talakawa saboda kyashi, amma basu san cewa yawan abin da kake bayarwa, yawan Albarkar da Allah zai maka ba.

Dangote ya bayyana haka ne yayin taron gidauniyar Florence Otedola Cuppy daya gudana a babban birnin tarayya Abuja, inda ya gabatar da jawabi a kan muhimmancin taimaka ma gajiyayyu mabukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel