Bayelsa: Kotu ta haramta wa dan takarar APC shiga zaben gwamna na ranar 16 ga wata

Bayelsa: Kotu ta haramta wa dan takarar APC shiga zaben gwamna na ranar 16 ga wata

A yayin da ya rage saura kwanaki uku a fita filin zabe domin kada kuri'a a zaben gwamnan da za a yi a jihohin Bayelsa da Kogi, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da APC daga gabatar da dan takarar gwamna a jihar Bayelsa.

A cikin hukuncin da kotun, a karakashin mai shari'a, Jastis I. E Ekwo, ta yanke, ta ce ta haramta wa jam'iyyar APC da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tsayar da 'yan takarar gwamna da mataimaki a zaben ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Kotun ta zartar da hukuncin ne biyo bayan karar da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, da mataimakinsa, Sanata Lawarence, Ewhruojakpo, suka shigar a gabanta.

Sun shigar da karar ne domin kalubalantar jam'iyyar APC, dan takararta da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a kan sahihancin dan takarar mataimakin gwamna a jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Gwarzon shekara: Wani matashi zai angonce da 'yammata uku rigis (Hoto)

Masu kara sun yi korafin cewa bai kamata a bar dan takarar mataimakin gwamna a jam'iyyar APC ya shiga takara ba bisa zarginsa da amfani da sunaye barkatai a takardun da ya mika wa hukumar INEC da jam'iyyarsa.

Da yake yanke hukunci a kan shari'ar, Jastis Ekwo, ya ce kotu ta gamsu cewa ba zai yuwu mutum daya yana amfani da sunaye daban-daban ba a kan takardunsa na karatu.

Wasu takardu da aka gabatar a gaban kotun domin kafa hujja sun nuna cewa, wanda ake karar na uku, wanda shine dan takarar mataimakin gwamnan sun nuna cewa yana amfani da sunaye 5 lokaci daya. Sunayen ne kamar haka:

1. Biobrarakum Degi-Eremienyo

2. Degi Biobarakuma

3. Degi Biobaragha

4. Adegi Biobarakumo

5. Degi-Eremienyo Biobarakuma Wanghagah, kamar yanda suke a takardun takara daban-daban da ya cike kuma ya mika wa jam'iyyar APC da INEC.

Bayan kotun ta dakatar da mataimakin daga yin takara, ta kuma hana dan takarar gwamnan yin takara tare da dakatar da jam'iyyar APC da INEC daga gabatar da wasu a zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar 16 ga wannan watan.

Kotun ta ce hukuncin ya shafi dan takarar gwamnan ne da jam'iyyar APC da INEC ne saboda ta hannunsu Degi-Eremienyo ya samu takarar mataimakin gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel